SANYA HAKORIN MAKKA A MA'AUNIN SHARI'A

SANYA HAKORIN MAKKA A MA'AUNIN SHARI'A



*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum Dr, dafatar ka tashi lafiya
Allah gafarta malam ina neman karin bayani game da Hauren makka da alhazzai suke sakawa akan cewa shima yana haddasa lum'a a lokacin da mutum ya zo kuskurar baki ruwa ba za su taba ainihin Hauren da Allah ya halicci mutum da shi ba?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam,

a zahiri sanya Haure bayan aikin hajji ba matsala ba ne ta fuskar Lam'a tun da kurkure baki sunna ne a wajan da yawa daga  malamai, wannan yasa rashin shafar ruwan ga hakori daya ba zai yi tasiri ba.

Amma zai iya zama matsala saboda yana iya janyo riya, tun da galibi wanda zai sanya yana yi ne saboda yaje hajji ko dan ace masa Alhaji, hakan ya sa barinsa shi ne ya fi.

Idan ya kasance an yi hauren ne da zinare to haramun ne namiji ya sanya saboda Annabi S.A.W. ya ce: (An haramta zinare ga mazajen Al'umata, amma an halatta ga matayansu)

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)