NASIHA A CIKIN MUTANE, TOZARTAWA NE



NASIHA A CIKIN MUTANE, TOZARTAWA NE
:
*TAMBAYA*❓
:
Asslamu Alaikum. Don Allah Mallam mene ne hukuncin wanda idan ya ga anyi kuskure yake tozarta mutum a cikin jama'a?! Shugaba ne na makaranta yake jan jam'i rana daya dalibi yaja da aka idar da sallah sai aka fara yiwa dalibin tozarta a gaban dalibai maza da mata kan cewa bai kamata ba, ni ina ganin da an kira shi gefe an masa nasiha da karin haske ko a hadasu iya maza ayi musu zai fi. Meye hukuncin haka? 
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum assalam, Yi wa mutum nasiha a cikin mutane bai dace ba, kuma hanya ce da za ta hana shi amsar nasihar, in ba wanda aka yiwa nasihar yana da tsananin ikhlasi ba, Annabi (S.A.W) yana cewa: 

*_"Wanda ya suturta Musulmi Allah zai suturta shi"._*

Kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2074.

*Allah ne mafi sani.*

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)