MAHAIFIYATA BATA AMINCEWA DA DUK WANDA YAZO NEMAN AURENA, MENENE MAFITA

MAHAIFIYATA BATA AMINCEWA DA DUK WANDA YAZO NEMAN AURENA, MENENE MAFITA





*TAMBAYA*❓
:
 Mallam tun inna karama babata suka rabuda babana. Yanzu haka shekarata 24 amma mahaifiya ta duk Wanda nakawo mata amatsayin miji saitaki yarda tace narabu dashi badan wai becika sharadin musulunci ba kawai dai ra'ayinta haka zan hakura saboda nayimata biyyaya to yanzu mallam nasamu wani me hankali da nitsuwa da addini amma shima taki. Shine nikuma nayanke shawara nafadama banana kuma yamince yace aure insha Allahu sai anyi itakuma ta rantse Wallahi idan tana raye baza ayi ba ko anyi saina haɗu da masifa tunda ita tadau nauyina maganganu dai marasa daɗi, to yanzu mallam meye mafita tunda babana ya mince kuma nima ina sonsa ita kuma tace ba yawunta.Kuma inason aure sosai.
:
*AMSA*👇
:
'Yar uwa wannan matsala ce da take bukatar shawarwari kamar haka:
1 .Yawaita adu'a, musamman Neman za6in Allah (istikhara) da fatan Allah yaganar/juyo hankalinta ta duba halin dakike ciki.
..
2 .Zuwa wajenta da nusar da ita akai-akai ta hanyar lafuza masu sauqi da daɗi.
..
3 .Idan tanada iyaye abiyo ta wajensu.
..
4 .Idan tanada qawaye (abokan)shawara nagari suma akwai bukatar sushiga.
..
5 .Kituro masoyin naki yakai mata ziyayara shi kaɗai aboye, kuma kar yaje hannunsa goma. Annabi (SAW) yana cewa: Kuyi kyauta zaku sami soyayya, kamar yadda ya tabbata a hadisi.
...
6 .Yatura 'yan'uwansa suje wajenta don nuna muhimmancinta akan wannan magana.
..
7 .Sai kuma Yawaita sallah, karatun Alqur'ani, istigfari da aiyuka nagari domin suzamo tsani gareki Allah ya amsa wannan bukatar.
..
Amma koda bata aminceba za'a iya yin aure saboda Annabi (SAW)yace: Ana biyayyane kawai cikin abu mai kyau, kamar yadda hadisi ya tabbatar.
         Sannan baya cikin sharadi wajen bada aure wai sai mai kuɗi, Annabi (SAW)Yace: idan wanda aka amince da addininsa da halayensa(nagari) yazo Neman auren 'yarku sai Ku aura masa, amma idan kunqi to lallai fitina zata bullo abayan qasa.
      Malamai sukace wannan fitinar bata wuce zinace-zinace da lalacewa da mata sukeyi saboda mugun kwadayi da dogon buri. Sunqi auren mutanen kirki don hangen abin duniya. Allah yasa mudace.
:
Allah ta'ala yasa mudace
:
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)