IGIYA NAWA NE YA RAGE WA MIJIN DA YA SAKE AUREN MATAR DA YA SAKI BAYAN TA AURI WANINSA ?

IGIYA NAWA NE YA RAGE WA MIJIN DA YA SAKE AUREN MATAR DA YA SAKI BAYAN TA AURI WANINSA ?



*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam Idan mace mijinta ya sake ta saki 2 ta fita ta yi wani auren can ma aka sake ta, to sai ta dawo gidan tsohon mijinta, me saki 2 din nan, ya matsayin sakin da ya yimata guda 2 a baya? Kuma na gode malam.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

Matar da mijinta ya sake ta saki biyu, lokacin da ta gama idda sai wani ya aure ta, daga baya shi ma ya sake ta, ko ya rasu, sai mijin can na farko ya dawo ya qara aurenta, to a yanzu igiyar aurenta da mijin farkon can ya zama saura igiya ɗaya ne ba uku ba, auren ta da miji na biyu ya yi ba shi da tasiri wurin canja lissafin igiyoyin aurenta da miji na farko, kamar yadda malamai suka bayyana.
Idan kuma lokacin da mijinta na farko ya sake ta igiyoyin aurensu dama sun qare, wato saki uku sun qare, to bayan ta auri miji na biyu, idan ya sake ta kuma ta gama idda, ko ya rasu, to a wannan yanayi idan mijinta na farko ya sake auren ta, igiyoyin aurensu za su zama guda uku ne cif, wato ta zama tamkar wacce bai taɓa auren ta ba kenan.
Don neman daɗin bayani a duba Almugniy (7/504, 506), ko a duba Assharhu Almumti'u Ala Zádil Mustaqni'i (13/197).

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)