MACEN DA BA A IYA SAKI 10

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(10)*
           
*WADA TUWA DA MAI GIDA*
    
       Ya "yar uwa mai Albarka ki sani yana daga cikin jin dadin duniya da lahira shine wada tuwa da mai gidanki, kada kyawunki ko matsayinki ko nasabarki tasa ki dunga hangen wani tare da raina matsayin mijinki saboda kin masa fintinkau. 
   Allah subhanahu wata'ala da kansa ya yabi matan Aljannah wajan siffanta su da cewa " A Aljannah akwai masu taqaitaccen gani ". 
   Haka Abdullahi bn Abbas yake cewa abun da ake nufi a wannan ayar "baza su ga wasu acikin Aljannah ba wadanda suka fi mazajen su ba". 
  An rawaito cewa :"mace daga cikin matan Aljannah idan taga mijinta sai tace wallahi ban ga wani abu acikin Aljannah ba da ya kai ka kyawu haka zalika babu abun da yafi soyuwa agareni sama da kai, nagodewa Ubangijin al'arshi da ya sanya na zama taka kaima ka zama nawa". 
 Haka zalika umama bnt haris tana yiwa "yarta nasiha ya yin aurar da ita tace ki wadatu da mijinki duk yadda yake". 
   Ya "yar uwa mai Albarka ki wadatu da mijinki duk yadda yake ki godewa ubangijin al'arshi akan haka wasu da yawa basu samu irin naki ba, ki girmama kyawunsa, haka zalika samunsa ko nasabarsa, tabbas "yar uwa mai Albarka babu yadda za'ayi ki dabi'antu da irin wannan dabi'ar saki ya ziyarci gidanki, hakan bazai yuwu ba sai dai kiji labarin sa a wani gidan ba naki ba, kuma kece mai nasarar da muke wa laqabi da macen da ba'a iya saka.
 
*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 11*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)