NA CI ABINCI , BAYAN ALFIJIR YA KETO !

NA CI ABINCI , BAYAN ALFIJIR YA KETO !


Tambaya :
Malam jiya bayan na gama cin abinci, sai na samu ashe alfijir ya keto, tun kafin na fara ci, saidai Allah ya sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu ?

 Amsa :
 To malam mutukar ba da saninka ka yi haka ba, to azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai azumi ya yi kokwanton huduwar alfijir, to ya halatta a gare shi ya ci abinci, saboda wanzuwar dare shi ne asali, kamar yadda Ibnu-abbas yake cewa : "Allah ya halatta mana cin abinci - a Ramadhana- mutukar mun yi kokwanton hudowar alfijir", saidai in da zai yi kokwanton faduwar rana to bai halatta a gare shi ya ci abinci ba, saboda wanzuwar ranar shi ne asali. 

Allah ne mafi sani

Jamilu Zarewa 
20\7\2014


Post a Comment (0)