LADUBBAN ADDU’A

LADUBBAN ADDU’A 



TAMBAYA❓
:
Assalamu alaikum, malam ina kwana yagida ya aiki dafatan komi lapia.
Malam tambayoyina anan sune:
1. Shin ko akwai wasu azkar wanda idan kayisu Allah zai amshi addu'arka da gaggawa kamar yankan wuka, duk da cewa shi Allah ba'ayi mashi gaggawa cikin lamurranshi amma dai abun ina bukatar taimakon gaggawa.

2. Shin musulmi da Christian suna da alfarmar da Allah zai amshi rokonsu kasancewar shi Arrahmanu?.

Allah yabada ikon amsa tambaya.
:
AMSA👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Idan mutum yana da wata bukata ana so ya kintaci lokacin da akafi amsar addua (kamar tsakanin kiran sallah kafin tada iqama, ko lokacin saukar ruwa, ko sa’ah na ranar Juma’a(wanda take farawa daga bayan La’asar), ko daya bisa uku na karshen kowane dare, ko a cikin sujjada ko karshen zaman tahiya(a sujjada da karshen tahiya an fi so a zabi addu’ar da ta tabbata a Qur’ani ko Sunnah wadda ta dace da bukatar da ake nema), ko bayan aikata wani aiki na alkhairi, da makamantan su).

Ana so mai addu’a ya ɗaga hannun sa ya kira Allaah da sunayenSa kyawawa da siffofinSa madaukaka(musamman sunaye da siffofin da suke da alaka da bukatarSa, misali idan yana neman arziki ne sai yayi amfani da irin Ya Razzaq, Ya Wahhaab, Ya Fattaah, Ya Kareem. Idan kuma ilmi ne sai ya haɗa da Ya Aleem, da makamantan sa), Yayi ma Allaah kirari ya yabe Shi da yabon da ya dace da girmanSa, sannan bawa yayi furuci da gazawarsa da bukatuwarsa zuwa ga Allaah, sannan ya godewa Allaah kan ni’imar da yake ciki, sannan ana so ya kira Allaah da ISMULLAHILLAHIL A’AZAM – wanda idan aka kira Allaah dashi ko aka roke Shi Yake amsa Ya biya bukata( kamar Yã Hayyu Yã Qayyūm, ko kuma; Allãhumma innī ash’hadu annaka antalLãh lã ilãha illã anta al’ahadus swamad allazhiy lam yalid wa lam yūlad wa lam yakun lahu kufuwan ahad), sannan sai yayi salati ga Annabi sallallaahu alaihi wa ala alihi wa sallam, sai ya fadi wa Allaah bukatan sa yana mai kudurce cewa Allaah Zai biya masa, bayan ya gama addu’ar sai ya sake yi ma Annabi salati s.a.w.
Zai cigaba da yin addu’ar har zuwa sanda Allaah Zai biya masa bukatar sa. Domin ita kanta addu’a ibadah ce, dan haka maimaita ta yana ƙarawa bawa kusanci ne ga Allaah madaukakin Sarki.

Sannan idan aka samu jinkiri wurin biyan bukata da aka roka; baya nuna Allaah Bai amsa addu’ar ba, a’a, domin amsa addu’a yana faruwa ta hanyoyi dadama:
1- Imma Allaah Ya amshi addu’ar Ya biya ma mutum bukatar sa a take.
2- Ko kuma Ya amshi addu’ar amma sai Ya jinkirta biyan bukatar saboda wata hikma da Shi Allah din kaɗai Yabar ma kanSa sani, watakil Allaah cikin ilminSa da gamammen saninSa Yasan idan Ya baka bukatar a wannan lokacin wata matsala zata same ka ko zaka haɗu da wata tangarɗa a rayuwa.
3- Wani lokaci kuma Allah Zai amsa addu’a amma sai Ya canza ma mutum da abunda yafi alkhairi gare shi, saboda a ilmin Allaah Yasan idan Yaba mutum wannan bukatar Zata zama sanadiyyar halakar sa, ko ta zama masa sharri maimakon alkhairi.
4- Wani lokacin kuma Allaah Yakan amshi addu’ar bawa amma sai Ya tunkude masa wani bala’i ko musifa dake tinkararsa, ko kuma ya kankare masa wasu laifukan sa madadin biya masa bukatar da ya nema.
5- Wani lokaci kuma Allaah Yakan amsa addu’ar bawa amma sai Ya tanadar masa da ladanta da kuma bukatar da ya nema, Ya bashi a Lahira, ko Ya daukaka darajarsa a Aljannah, ko Ya kare shi daga shiga wuta a dalilin addu’ar.
6- Ko kuma Allaah Yana so ne ka zama ɗaya daga cikin bayinSa na kusa daShi, shi yasa Bai biya maka bukatar ka a take ba, saboda ka cigaba da da addu’a domin ƙara kusanta gareShi.
Dan haka rashin samun bukatar da aka nema wurin Allaah baya nuna rashin amsar addu’ar bawa, domin amsar addu’a Yana samuwa ta ɗaya daga cikin ababe ko hanyoyin da aka ambata, wadanda bakidayansu suna da da madogara a nassoshi na Qur’ani da Sunnah.
Sannan Baya halatta mutum ya roƙi Allaah abunda Allaah Ya hana ko Ya haramta ko Yaya tsawatar, msl kamar mutum ya roƙi Allaah akan cutar da ɗan’uwan sa, ko ya roƙi Allaah Ya sa ya ƙware wurin sata ko zamba ko maguɗi, ma’ana dai ba a roƙon Allaah akan saɓa maSa.
Sannan ita addu’a an fi so mutum yayi ta dakan shi, amma babu laifi ya faɗa wa wasu(musamman salihan bayi) su taya shi da addu’a, amma nashi tafi muhimmanci. Sannan ana so mutum Ya nemi iyayen sa su rinƙa yi masa addu’a. Sannan ana so mutum Ya tuba ga Allaah tuba ta gaskiya da nadama daga zunubbansa da laifukan sa kafin addu’a. Sannan idan ya zalunci wani lallai ya nemi yafiyar sa, in kuma hakkine to ya maida masa.

Sannan:

Ba a hada Allaah da wani wurin roƙo.
Ta’ammuli da haram yana hana amsar addu’ar bawa.
Allaah Baya amsar addu’ar mai cin haram, ko shan haram, ko mai sanye da tufafi na haram.
Ba a son gaggawa gameda addu’a, misali bawa yace ina ta addu’a amma Allaah Bai amsa mun ba.
Ana son halarto da zuciya lokacin addu’a, da ƙanƙantar da kai ga Allaah SWT, domin Allaah Baya amsar addu’ar gafalalle.

✍🏻Rubutawa: Abdullahi Almadeeniy Kagarko.


Post a Comment (0)