KA NEMAWA ƳAƳANKA KARIYAR ALLAH DAGA CUTARWAR SHAIƊAN
Hanya mafi girma ta samun kariya daga sharrin SHAIƊAN shine ambaton Allah da addu'a kamar yadda Allah da Manzonsa suka koyar da mu, shi ya sanya Manzon Allah SAW ya koyar da mu nemawa ƴaƴan tsari daga cutarwar SHAIƊAN a lokacin saduwa da Iyali,ta hanyar fadar wannan addu'a:
[باسْمِ اللهِ،اللهمَّ جَنِّبْنا الشَّيطان]
*_BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAIƊAN,WAJANNIBISH SHAIƊANA MA RAZAƘTANA_*
Za'a faɗane lokacin kusantar Iyali
•┈┈┈┈•✿❁✿•┈┈┈┈•
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
(Da ɗaya daga cikin su zai faɗa a lokacin da ya zo saduwa da iyalinsa sai yace:-
[باسْمِ اللهِ،اللهمَّ جَنِّبْنا الشَّيطان]
*_BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAIƊAN,WAJANNIBISH SHAIƊANA MA RAZAƘTANA_*
Domin idan Allah ya ƙaddara masu samun yaro a wannan saduwa,SHAIƊAN ba zai cutar da shi ba har abada).
@البخــاري (6388) ومســلم 1434]
═══════════
القاضـي عيـاض رحـمـه الله:
Yace:-
Abin da ake nufi da SHAIƊAN ba zai cutar da shi ba, *shaiɗan bazai cutar da shi ba a lokacin haihuwa ba, kuma bazai cutar da rayuwar sa ba, ba ana nufin bazai sanya masa wasi wasi ba ko ruɗansa ba*.
@نقله النــووي في شــرح مســلم 10/5[
═══════════
*_SHIN MIJINE KAƊAI ZAI FAƊI WANNAN ADDU'AR LOKACIN SADUWA KO HAR DA MATAR??_*.
العلّامــة ابن عُثيمين -رَحِمهُ الله
Yana cewa:-
"abin da Yake a zahirin wannan hadisin shine:-
*Miji shi yake da hakkin fadar wannan addu'a shi kadai domin Allah yana halitta ne daga ruwan namiji, amma idan dukan su suka fada babu laifi_*
@شـرح صـحيح المسلم ٣١/٥〗
═══════════
*_WANDA YA MANTA BAI YI WANNAN ADDU'AR BA LOKACIN SADUWA??_*.
الامـام الالبـاني -رَحِمَهُ اللهُ- :
Yana cewa:-
Wanda yake yawaita yin wannan addu'a duk lokacin da zai sadu da iyalinsa yana faɗa dan ya manta lokaci guda bai faɗa ba to Insha Allah shaiɗan bazai cutar da abin da za'a haifa ba saboda tasirin wannan addu'a kuma shaiɗan bai yi tarayya da shi ba cikin saduwa da iyalinsa ba.
@سلــسلة الهــدى والنــور 12 ب〗
•┈┈•┈┈•⊰✿📚✿⊱•┈┈•┈┈•
Abu mafi tsoro shine:-
Rashin faɗar wannan addu'a lokacin saduwa yana janyo illoli guda uku manya:-
*Samun tarayya da SHAIƊAN cikin saduwa da iyali*
*CUTARWAR Shaiɗan ga abin da aka samu na rabu*
*Rashin aiki da sunnar Manzon Allah SAW*.
Allah ne mafi sani
*_Allah ya bamu ikon kiyayewa ka bamu zuri'a ta kwarai kuma ka kare mu daga sharrin SHAIƊANUN ALJANNU DA NA MUTANE_*.
Tnx you
ReplyDelete