AIKIN DA ZAKAYI KA SAMI LADAN WANDA YAYI HAJJI DA UMRA

AIKIN DA ZAKAYI KA SAMI LADAN WANDA YAYI HAJJI DA UMRA


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum
Wani aikine nutum zaiyi Allah yabashi ladan haji da umara
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salamu warahmatullah.

Suna da yawa, kadan daga ciki:

1. Annabi ﷺ yace: ( WANDA YA SALLACI ASUBA ACIKIN JAM'I [jama'a], SANNAN YAZAUNA AWURIN YANA ANBATON ALLAH HAR RANA TA FUTO, SANNAN YA SALLACI RAKA'A BIYU [na nafila] TA KASANCE AGAREAHI TAMKAR HAJJI DA UMRAH)
Anas yace: Manzon Allah ﷺ CIKAKKU). wato Hajji da Umra
Sunanut Tirmiziy: 586.

2. Annabi ﷺ yace: ( DUK WANDA YAFITA DAGA GIDANSA DA ALWALLA ZUWA GA SALLAR FARILLAH [jama'a], TO LADARSA KAMAR LADAR MAI MAHARRAMA DA HAJJI).
Sunanu Abi dawud: 558

3. ( WANDA YAFITA DAGA GIDANSA ZAIJE SALLAR WALHA [duha], BA ABINDA YAFITAR DASHI SAI ITA, LADARSA KAMAR LADAR MAI UMRA NE).
a duba:Sunanu Abi dawud:558.

Daga Abu Umamah Allah yakara masa yarda.

4. Annabi ﷺ yace: ( SALLAH ACIKIN MASALLACIN KUBA,  TAMKAR UMRA CE).
a duba:Sunanu Ibnu Majah:1411.
a duba:Tirmiziy:324.

5. Dabtaniy yaruwaito acikin Al ausad Annabi ﷺ Yace:
( IDAN MACE NA GIRKI, TANA KAI KOMO TSAKANIN DAKINTA DA MADAFI [kiching , domin dauko gishiri mai dadai sauransu], TO ANA BATA LADAR SAFA DA MARWA NE).

6. Ana cewa: Annabi ﷺ yace: ( IDAN MACE TAYI KWALLIYA TA KWANTA KAN GADON MIJINTA TANA JIRAN DAWOWARSA, TO TANA DA LADAR HAJJI DA UMRA).

Karin bayani

❗1. Zuwa masallaci jam'i na jawo ladar aikin hajji.

❗2. Zuwa masallaci sallar walha na kawo ladar Umrah.

❗3. Zama bayan sallar asuba ana zikiri na sunnah ba atashiba, ba ayi magana ba, ba'ayi bacci ba, ba ayi tusa ba, har rana tafito ,kuma akayi sallar hantsi raka'a biyu, na sa a Samu ladar Hajji da Umrah ga baki daya.

❗4. Mata masu daukar yar aiki tana yi musu abinci suna yin hasarar Safa da Marwa.

❗5. Kwalliya asa turare ajira mai gida akan gado yana sa asamu hajji da umrah.

❗6. Maziyarta madina suyi kokarin sallah a masallacin kuba, inkun kara sati daya.A madina  sai kukoma, domin Annabi duk mako yake zuwa, amma ba dole sai kayi alwallah daga gida ba.

❗7. Mata marasa aure, ansha dasu, anyi masu fintinkau, Allah sarki.

AMSAWA
SHAFI'U SHEHU MINNA
(08033410797)

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)