HUKUNCI AMFANI DA MOTAR OFFICE A HARKOKIN KASHIN-KAI ?

HUKUNCI AMFANI DA MOTAR OFFICE A HARKOKIN KASHIN-KAI ?


*TAMBAYA*❓
:
Assalama alaikum Malam ya halatta mutum ya zuba mai a motar ma'aikatar da yake aiki, ya kai matarsa unguwa, ko ya je harkokinsa na yau da kullum, a ciki ?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam

To dan'uwa kwamitin fatawa na din-din na Saudiyya ya bada fatawa cewa: Bai halatta mutum ya yi amfani da motar gwamnati wajan harkokinsa na yau da kullum ba, tunda ba dan haka aka tanaje ta ba, kamar yadda ya zo a fatawa mai lamba ta: 16594.

Sheik Ibnu Uthaimin yana cewa: "Ko da shugabanka na office ya halatta maka, bai halatta ba, tun da ba huruminsa bane, ba kuma mallakinsa bane, kamar yadda ya zo a Lika'u babil maftuh: 238.

Yana daga cikin siffofin muminai kiyaye amanar da aka damka a hannunsu, kamar yadda aya ta: 8 a suratul Muminuna ta tabbatar da hakan.

An rawaito cewa Khalifa Umar dan Abdul'aziz ba ya amfani da fitilar gwamnati a harkokinsa na kashin-kai, ko da kuwa bako ya yi bai zai yi hira da shi da fitilar gwamnati ba, in har ba matsalolin da suka shafi jama'a za su tattauna ba, wannan sai ya nuna taka-tsantsan da dukiyar office yana daga cikin tsentseni.

Duk wanda ya wadatu Allah zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da ba ta karewa.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)