Fifiko mafi DARAJA, shi ne fifikon tsoron Allah
Allah Ta'ala ya jik'an Mal. Ja'afar Mahmud a Karkashin wani Hadithi yake cewa, mutane biyu suke rayuwa:-
1- Mai tsoron Allah mai (Taqwa) bin dokokin Allah
2- Maras bin dokokin Allah, (mai biyewa son zuciya..
Idan ka fito a na farko, ba shakka ka tsira, kuma kaine mai matsayi mai daraja, (masoyin Allah) se ka shiga cikin Wanda Allah swt ya ce: "Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) Wanda yake mafificinku a tak'awa.."
Idan ka fito a na biyu, (maras taqwa) mai biyewa son zuciya da duniya, ba shakka, Kaine maras kima, Kaine wulak'antacce, kome ka ke da shi na duniya.
Allah Ta'ala ka dauki rayukan mu kana mai yarda da mu. (Amin)
✍️ *Salma Nakumbo Kazaure*