INA NEMAN SHAWARA AKAN SOYAYYA DA WATA BAIWAR ALLAH

INA NEMAN SHAWARA AKAN SOYAYYA DA WATA BAIWAR ALLAH.


https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
:
*TAMBAYA*❓
:
Slm. Amincin Allah SWA tabbata agareka ya Mal. Ina Mai addua Allah yakara ilimi DA imani DA Kuma takwa ya Kuma albarkaci xurriyya ameen. 

Mal. Kamar shekara daya data gabata DA akwai wata yarinya data ganni tace tana Sona Kuma tacemun ita Dan Allah idan ina santa infadamata ammafa insani ita soyayyar aure take nufi Ba soyayyar Yan xamani ba (sayayyar Jin Dadi).
Sbd tadade tana karatu game da halayena DA dabiuna dakuma addinina shiyasa taga yadace ta xabeni amatsayin uban yayanta. 
To Mal alokacin wlh banyi wani dogon tunaniba Kawai Saina amshi soyayyarta. To yanxu abunda nake fadamaka wlh Mal ankai kudin aure Kuma ansa rana wata biyar DA suka wuce yanxu haka auren saura wata hudu. To Amma Mal. Damuwar tawa itace wlh Mal yarinyar addininta,iliminta Na xamani dana addini DA Kuma tarbiyyanta yayimun wlh mal. Asanadiyyarta DA Bana fita Sallah r asuba Amma yanxu kullun Saina flta sbd tana kirana awaya tace Na tafi masallaci Har Na ma Saba. 
To Amma Mal. Wlh yanxu yarinyar DA yake Allah yayita Mai karamin jiki Kuma gajera. wlh Sai nakejin gaba Daya yanxu wlh Mal. Gaba Daya yanxu idan Na kalleta kwata kwata banajin Wani shauki Ko kaɗan Na soyayyar ta wlh mal. Yanxu ahalin danake ciki Ko kadan Naji banasanta sbd ina ganin Bata DA qualities na jiki Mai Girma DA Kuma Sura(Diri) Ni Kuma Gani Allah yayini Mai babban jiki shine Har Sai Kaji wasu mutane(Yan UWA Ko abokai) suna cemun Kai wannan yarinyar xaka aura Ai tayimaka kankanta Tom shine nake ganin Mal ina bukatar nasiha, (Waaxantarwa), DA kuma mafita akan Hakan sabuda ina tsoran Kar ayi auren yaxama ansamu matsala. 
Mal. Mene mafita.?
Allah yasakawa Mal DA mafificin alkhairi. 
Ya jikan hajiya.

:
*AMSA*👇
:
 Kowanne Namijin yana da Classification da kuma Test na mace mai Irin Suffar da Kirar da yake burin ya ga ya aura. Ma'ana mai irin surar da ta kwanta Masa a Ransa. Shiyasa ma Allah Ya halicci Mata iri-iri. Wata doguwa, wata gajera, wata fara, wata Baka, wata kuma wankan Tarwada.
 Wani Lokacin irin wannan da kai kake ganin Baka so, wani kuma Irin ta yake so.
 Amma duk da haka ba zaka ce bata yi maka ba. Sabida Addinin ta. 
 Manzon Allah saw Yace KU AURI MA'ABOCIYAR ADDINI, ZAKU CI RIBA. Ma'ana zaku ci Ribar zama da su, haka zalika Zaku ci Ribar Lahira. Wanda gashi tin ba aje ko ina ba, ka fara cin Ribar Lahira ta dalilin wannan Baiwar Allah din. ma'ana gashi tin yanzu tana tashin ka, ka tafi Masallacin Asubahi. Daga ji wannan Baiwar Allah Akwai Alkairai a Tattare da ita. 
  Sannan kuma Allah da kansa yana cewa DA SANNU ZAKU KE SON WANI ABU, ALHALIN WANNAN ABIN SHARRI NE A GARE KU. SANNAN KUMA DA SANNU ZAKU KE KIN WANI ABU, ALHALIN KUMA WANNAN ABIN ALKAIRI NE A GARE KU, ALLAH SHINE YA SANI, AMMA KU BAKU SANI BA.
 Sabida haka karka ki Wannan Baiwar Allah din. Ka Kaddara a Zuciyarka Kaci karo da Abinda kake Rokon Allah ya Baka. Matukar dai kana yin Addu'a a baya. Domin Zaka ga Wani ya dage da yin Addu'a Allah ya bashi Mace ta Gari, sai ya samu kuma sai kaga yana ganin Kamar akwai wani Nakasu. Wanda kuma Samun Mace ta Gari Yana daga cikin Arzikin Duniya da Lahira.
 Sabida haka kenan. Shawara ta shine. Ka kwantar da Hankalinka. Insha Allahu Alkairi ne Aurenka da Wannan Baiwar Allah. Sabida irin ta ce manzon Allah saw ya Baka Zabi. Ma'ana Ma'abociyar Addini.
 Kar ka Jefa kanka cikin Matsala. Ma'ana kar kayi Auren Sha'awa. Auren Sha'awa shine Auren Da na sani.
  Matsalar mu Maza shine. Zaka ga Mutum Bakin Kirin da shi, Amma fa da ya tashi yin Aure, sai Yace Shi ba zai auri kowacce irin Mace ba sai Fara tas. Kaga tin daga Nan Wannan Bawan Allah ya Fara Baiwa Aure Wahala.
 Haka zalika, za kaga Mutum gajere da shi, dan Dukurkushi. Amma sai Yace shi ba zai auri mace ba sai Doguwa. Ko Zance yaje wajen ta sai ya Hau kan Wani Abu dan ta ga cewar Shi mai tsawon ne. Kaga wannan ma tin daga waje ya fara Baiwa Aure Wahala.
Wani za kaga wani. Shi kansa Bashi da wani kyau (Afwan), Amma sai ya Duba Yarinyar da tafi kowacce mace kyau a Unguwa. Sai Yace Shi ita yake so. Harma idan yaji Ance wa ne yana son ta. Sai ya fara yiwa wannan Mutumin gaba, ya dena yimasa magana. Sabida Wai yayi masa kutse a cikin soyayyar sa. Kaga wannan ma ae tin daga waje ya fara Baiwa Aure Wahala.
 Wata Matar, ba kyawun ka bane kyau a wajenta. Kuɗin ka shine kyawunta. Da zarar an wayi Gari Baka da wannan kuɗin. Mummuna zata ke ganinka. 
 Sabida haka, ka Kwantar da Hankalinka, ka yarda da cewar wannan matar zabin Allah ce a gareka. Shikenan ka huta.
 Kuma In Banda abinka. Kai da kaga matar Nan Kace kana Sonta. Har ma kun Shaku da Juna, har ka kai kayan Aurenka gidansu. Kana Nufin, zuwa zaka yi kace ka Fasa Kenan? Sabida Maganganun Mutane. Ka Fita harkar Mutane. Wasu Mutanen basa fatan Alkairi, sai Abinda ba na Alkairi ba. Idan ka biyewa Mutane. Zaka Halaka. Kabi Umarnin da Allah ya yiwa Annabin wannan Al'ummar cewar "IDAN KA TASHI ZAKA YI WANI ABU, KAYI TAWAKKALI GA ALLAH".
 Su Mutane, idan Alkairi ya same ka. Sai ka ji suna ta Surutu. Idan kuma Sharri ne ya same ka. Sai kaji sunyi Shiru. Ka Fita harkar wadanann Mutanen. Kawai kayi Aurenka.
 Allah ya Baku Zuri'ah ta Gari.

Allah Shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797

GROUP ADMIN:👇
Mal. Khamis Yusuf
+2348087788208
+2348054836621

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)