MIJINA BA IYA BIYA MIN BUKATA, MENENE SHAWARA ?
*TAMBAYA*❓
:
Assalamun alaikum, Malam mace ce mijinta ba ya iya biya mata bukata saboda raunin mazakutarsa, kuma ashe abin da ya raba shi da uwar gidansa kenan.
Kasancewar ba ya biya mata bukata ta shiga cikin halin damuwa, sannan ta yanke shawarar cewa: in ya kira ta shimfidarsa ta daina zuwa, to malam ta yi laifi game da wannan shawarar da ta yanke ?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam,
A shawarata kamata yayi a kira magabatansu su zauna su tattauna a gano yadda za'a warware matsalar.
Idan har ya tabbata ba cikakken namiji ba ne to za'a bashi shekara ɗaya ya nemo magani.
Idan ya warke shikenan, in bai warke ba kuma za ta iya fadawa cikin haram idan taci gaba da zama dashi, to ya halarta a raba auran, kamar yadda aka raba da uwar gidan.
Yana daga cikin manyan manufofin aure: ma'aurata guda biyu su katange junansu daga haram, in har aka rasa wannan to akwai matsala a zamantakewar aure.
Allah ne mafi sani.
*Dr, Jamilu Zarewa*
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ