MACEN DA BA A IYA SAKI 11

MACEN DA BA'A IYA SAKI............



🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(11)*
       
*KI KAUNACI ABUN DA MAI GIDANKI YAKE KAUNA*

   Ya "yar uwa mai daraja kiyi kokari wajan nisantar yin adawa da nuna tsantsar kiyayya da abun da mijin ki yake so, kiyi mu'amala da wannan abun tare da nuna kauna ta gaskiya gare sa, ko da yaushe ki dunga duba ban garen amfanin abun, domin 
kallon ban garen rashin amfanin abun na iya jawowa Rayuwar Auratayyyar ku kunci da damuwa.
   Wata rana wani Aboki ya bawa abokinsa littafi domin ya karanta, wa she gari sai ya dawo masa da littafin sai yace ya karanta, sai abokin nasa ya yi mamaki wajan saurin kammala wannan karatun da ya yi cikin dare daya, sai ya tambaye shi ya akai ka iya karanta wannan littafin da wuri haka bayan jiya mun dauki tsawon dare muna hira tare da kai? Sai ya yi murmushi yace ya kai aboki na kasani bani na karanta littafin ba mata tace ta karanta, sai yace dashi matar ka kenan tana san karatu, sai yace a a sai ya yi murmushi yace lokacin da na aure ta, na gaya mata cewa karatu yana daga cikin abubuwan da nake so kuma nake qauna, daga wannan lokacin ta lazimci horar da kanta karatu, har takai tana iya zama ta dau tsawan lokaci tana karatu sama dani. 
   Ya "yar uwa mai daraja ki bawa kanki amsa shin wannan bawan Allah zai iya rabuwa da wannan baiwar Allah kuwa? 
   Haka zalika mutuqar kika matsa wajan nuna adawa da abun da mai gidanki yake qauna tabbas hakan zai haifar maki da rikici da rashin samun kwanciyar hankali acikin gidanki. 
    Don haka yar uwa mai daraja kiyi kokari wajan qaunar abun da mai gidanki yake qauna domin ki Kasan ce cikin mata yen da muke wa laqabi da macen da ba'a iya saka.

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 12*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)