DAGA CIKIN ALFANUN YAƘIN RUSSIA DA UKRAINE

DAGA CIKIN ALFANUN YAƘIN RUSSIA DA UKRAINE:


Jihadin da ake yaƙi da shi sai gashi yanzu ya zama tirjiya da gwagwarmaya, ƙunan bakin wake ta zama jarumata, girmama dokoki da majlisa ɗinkin duniya sai gashi duk an watsar da su, haƙƙin dan Adam ɗin da yake zama ma'aunin sassaucin ra'ayi ko tsattsauran ra'ayi shima an take shi, a taƙaice dai duk wasu gumakan da Turawa suka sassaƙa suke ƙoƙarin lallai sai sun tilastawa musulmai sun bauta musu duk sun watsar da su sun cinye su !! Kamar dai abinda muke karantawa muke mamaki game da ƴan jahiliyyar farko da suke ssassaƙa gumaka da dabino in sun ƙoshi su bauta musu in sun ji yunwa su cinye su sai gashi yana maimaituwa a ƙarni na 21 a gaban idanmu!! Gane wannan yana daga cikin manyan alfanun wannan yaƙi na Russia da Ukraine.

Babban asararre kuma shine wannan gafalallen musulmin da bai taɓa ƙoshi ba balle ya yi bautar da hujja kullum cikin yunwa yake amma kullum ƙara nitsewa yake a bautar waɗannan gumakan na Taruwa yana mai hukunta ƴan uwansa da su!!

#Abdurrahman Muhd Sani Umar 
.
.
FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)