SAI KIN YI HAƘURI



'Yar uwa! A irin wannan lokaci na zafi, sanya Hijabi wadatacce sai kin yi hakuri, sai kin jure Zafi da zufa. To amma a duk lokacin da irin wannan zafin ya nemi ya sa ki cikin ruďani, ki dinga hasashen irin zafin Wutar jahannama wadda za ta kasance makoma ga masu bayyana tsiraici, Shin kin yarda ki guje wa Zafi a duniya a lahira kuma a tsunduma ki a Wuta? Lallai ki kasance mai sanya Hijab don neman yardar Mahaliccinki ba don qawata jikinki kawai ba, tuna cewa; Allah ne Ya yi umarni da sanya hijab, don haka ki ďauke shi a matsayin ibada, kada ki ďauki huďubar shaiďainun mutane masu kokarin nisanta ki da Mamallakin wuta da aljannah, kuma kada ki yi koyi da waďanda suka sayi 6ata (astray) da shiriya. 

Wannan tunatarwa ce ga masu tunani 👌 

*✍🏿Ayyub Musa Jebi.*
*(Ansar).*
*May, 2020.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*
Post a Comment (0)