HUKUNCIN MASU KIRKIRAR LABARIN KARYA DON SU BAMA MUTANE DARIYA (COMEDIANS)
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu
Malam don Allah menene hukunci wandanda suke Kirkirar labarin karya wai don su bama mutane dariya?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salam warahmatullah.
Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace :
( AZABA TA TABBATA GA WANDA ZAI BADA WANI LABARI SAI YAYI KARYA DOMIN YADARIYANTAR DA JAMA'A DASHI, AZABA TA TABBATA AGARESHI, SANNAN AZABA TA TABBATA AGARESHI).
Tirmizi yaruwaitoshi acikin كتاب الزهد (kitabus zuhudi) babi na 10.
Abinda yazo gameda Wanda zai furuta wata kalma domin yasa mutane dariyata dubi: Hadisi na 2315.
a dubi: Abu dawud:4990.
a dubi:Sahihul jam'i:7136.
daga:
Bahazu bin Hakim daga Babansa daga kakansa (رضي الله عنهما)
⚫Kamar masu karatun Ruwan bagaja
⚫Iliya Dan Mai karfi novels ,
⚫da masu rubutawayda
⚫ masu karantawa da
⚫ masu yi da baki duk sun shiga cikin wannan hadisin.
Allah ya kare mu da karya ko wace iri ce.
والله تعالى أعلم
SHAFI'U SHEHU MINNA
(08033410797)
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ