SHIN MALA'IKU SUNA SHIGA GIDAN DA AKWAI HOTO A CIKI?

*TAMBAYA*❓
:


SHIN MALA'IKU SUNA SHIGA GIDAN DA AKWAI HOTO A CIKI?
:
*AMSA*👇
:
Yabo ya tabbata ga Allah.
To ɗan uwa mala'ikun da suke ricodin din aiyukan bayi suna shiga gidan da akwai hoto. Idan akace duka basa shiga kaga kenan sai mutum yayi barnarsa ba tare da an rubuta masa zunubi ba, sai abin ya zama wasa kenan, to malaman da suka ce ba duka ba wannan tana daga cikin hujjarsu, amma dai biyo ni don mu duba sauran bayanai.

Da farko wane mala'iku ake nufi waɗanda ba sa shiga gidan da akwai hoto a ciki?

Al Imamul Bukhaari (3226) da imam Muslim (2106) sun ruwaito hadisi daga Abu Talhah (Allah ya ƙara masa yarda) cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce; “Mala'iku basa shiga gidan da da akwai hoto acikinsa.”

Al Imamul Nawawi (Allah yaji kansa da rahama) ya ce: Malamai sun ce: Dalilin da ya sa basa shiga gidan da akwai hoto acikinsa saboda akwai zunubi mai raɗaɗi, kuma gasa ne da halittar Allah, kuma wasu hotonan hotona ne da ake bautarsu maimakon Allah. Ga me da mala'ikun da basa shiga gidan da akwai kare a cikinsa ko hoto, to sune mala'ikun da suke zuwa da rahama, albarka kuma suke rokarwa bayi gafara. Ga me da Mala'ikun da suke recodin din aiyukan bayi, suna shiga ko wane gida kuma basa taɓa rabuwa da ɗan adam a ko wane hali, saboda aikinsu shi ne rubuta aiyukan bayi kawai.

Sharhin hadisin Muslim, 14/84 ya ce Tuhfat al-Ahwadhi (8/72): Kalmar “Mala'iku basa shiga” yana nufin: mala'ikun rahama, ba mala'ikun recodin ba ko mala'ikun mutuwa.

Ibn al-Atheer (Allah ya yi masa rahama) ya ce: Abin da ake nufi shi ne mala'ikun da suke yawo ba mala'ikun ricodin ba ko wadanda suke nan a lokacin mutuwa ba.

A cikin Al-Nihaayah, 4/789. Imamu Suwiti (Allah ya yi masa rahama) ya ce:
Al-Khattaabi ya ce: abinda ake nufi shi ne mala'ikun da suke kawo rahama da albarka, ba masu rubata aiyuka ba.

Sharhin littafin al-Nasa’i, 1/141
Shaykh Muhammad ibn Ibrahim (Allah ya yi masa rahama) an tambaye shi: shin maganar sa akan “Mala'iku basa shiga gidan da da akwai hoto ko kare” Ma'anarsu daya a ma'ana kuma shin sun haɗa da mala'iku masu ricodi ko kuwa a'a? Sai ya amsa da cewa: da alama cewa ba su haɗa da wannan ba.

A cikin Fatawa wa Rasa’il Muhammad ibn Ibrahim, 1/169
Hotonan da suke hana mala'iku shiga gidaje hotona ne da suke da rai (wato zanen abin da yana da rai ko motsi), baya ga hotona da ake sawa na rashin ɗa'a.

Al-Khattaabi (Allah ya yi masa rahma) ya ce: Mala'iku basa shiga gidan da da akwai kare ko hoto da aka haramta ajiye shi. Ga me da wanene ba'a haramta ajiyewa ba, shi ne kamar kare don farauta, noma ko gadin dabbobi, ko hotona wadanda babu rai a jikinsu, kamar carpets, pillow wanda zaka ga akwai zanen flower ajikinsu, mala'iku basa hana su shiga.

Tuhfat al-Ahwadhi, 8/72 Shaykh Ibn ‘Uthaymeen ya ce: Idan hotonan an bi da su da daraja, kamar hotona akan carpet ko pillow, to mafi yawan malamai suna ganin cewa ya halarta.

To ɗan uwa bisa waɗannan hujjoji da maganganun maluma, mala'iku ba'a hana su shiga wani huri, saboda idan an haramta musu shiga to da wancen damar ba'a halarta ta ba.

Liqa’ al-Baab al-Maftooh, 85/6 ga me da salla a wurin da akwai hoto, baya halarta, har sai dai idan musulmin dole aka yi masa kuma aka hana shi cire hoton.

Malaman committee din fatwa su ka ce: Salla a wuraren da da akwai hoto be halarta ba sai dai idan akwai wani dalili. Haka mai yin salla da hoto a jikin rigarsa hotonan dabbobi, shi ma baya halarta ya yi salla da wannan tufafin, amma idan ya yi to sallar sa ta yi amma ya aikata haramun, saboda haka dole ne ya yi istigfari akan hakan. Fatawa al-Lajnah al-Daa’imah, 1/705

ALLAH NE MAFI SANI.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)