JANA'IZAR KARE

JANA'IZAR KARE


A wani gari ne akayi wani mutum mai kudi sosai sunansa mallam Sadi. Yanada kudi baida iyali sai wani katon bakin karen sa. Saboda son dayake nunawa Karen har anfara zarginsa akan watakila Karen na tsafi ne. Rana daya sai aka wayi gari Karen ya mutu, toh abunka da mai kudi sai yatara yan unguwarsu yace ayiwa karensa
jana'iza kamar yanda akewa mutane.
Aka taru anawa Karen jana'iza sai labari yaje kunnen sarkin garin. Sarki ya taso cikin baccin rai yazo kofar gidan attajirin nan da dogaransa. Yana zuwa ya fara fada kamar haka:
Sarki: "kai awane gari kataba ganin anyiwa kare jana'iza?" Yafada cikin fushi.
Attajiri: "Ranka yadade dama Karen nan ne kafin ya mutu yace inya mutu akayi jana'izarsa to abaiwa sarki miliyan biyar jama'a kuma abaiwa kowa miliyanbiyu biyu.
Sarki: cikin rawar jiki ya amsa "Wato shi marigayi din ne yafadi hakan?"
Attajiri "Eh"
Sarki: "Toh Allah Ya jikan Malam kare, maza mu kaishi makwancinsa. Hahahahaha.
Duk wanda yakaranta shima anbashi miliyan biyu!
Post a Comment (0)