KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 01

KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 01


.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
                  GABATARWA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga bawansa, Manzonsa kuma baɗaɗinsa Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa da kuma waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar tashin Alƙiyama.
.
Bayan haka, tilas ne ga kowane musulmi ya doge wajen godiya ga Ubangiji (TWA) saboda ɗumbin ni'imomin da ya yi masa. Allah shi ne ya ƙagi halittarsa, alhali kafin hakan (mutum) bai kasance wani abu abin ambato ba. Bayan nan kuma Allah (S.W.T) ya kyautata halittar ɗan'adam, ya sanya shi mai iya magana, mai hankali, mai tunani da rarrabe al'amura.
.
Ya kuma hore masa ni'imomi waɗanda ba za su ƙirgu ba, ga irin su ruwa, tsirrai iri-iri, dabbobin ni'ima, ƙasa shimfiɗaɗɗiya da kuma cikakkiyar damar sarrafa rayuwa daidai gwargwadon abin da aka ƙaddara masa. Ga kuma uwa uba ni'imar da ya yi mana na kasancewa musulmai, cikin al'ummar Manzon Allah, Annabi Muhammad (S.A.W).
.
Kamar yadda Allah ya halicci bil'adama, haka kuma ya ƙididdige rayuwarsa, ba kawai da ƙirgen shekaru ko watanni ba, a'a har ma bisa yadda zai sarrafa lokutansa a nan duniya, sannan ya karɓi sakamakon ayyukan da ya gabatar a gobe Alƙiyama. Bisa wannan dalili ne shuɗewar lokaci da zamuna suka kasance wasu abubuwa masu matuƙar amfani da izna a rayuwar ɗan'adam.
.
Sannan kuma addinin musulunci ya zo da cikakken tsarin gudanar da rayuwar ɗan'adam wanda ya game dukkan ɓangarorin rayuwa, sannan kuma ya dace da kowace nahiyar duniya da kowane zamani da mutum ke rayuwa ciki. Hukunce-hukuncen musulunci sun mamaye rayuwarmu baki ɗaya, babu wani abu da zai kasance a doron ƙasa face musulunci ya yi tanadi a kansa.
.
Duk da kasancewa zamani ya kawo manyan canje-canje na hanyoyin da mutane ke sadarwa a tsakaninsu, alal haƙiƙa addinin musulunci bai gushe ba sai ya samu ta cewa a wannan fage.
.
Don haka ya wajaba ga malamai su bijiro da hukunce-hukuncen da addinin musulunci ya yi tanadi yadda ya kamata a tunkari al'amarin sababbin kafofin sadarwa da abubuwan da suka kunno kai na tagomashi da ma ƙalubale da amfani da sababbin kafofin zamanin suka kawo mata.
.
Bisa la'akari da irin ƙalubalen da ke tattare da sababbin kafofin sadarwa na zamani da tasirin da suke haifarwa a rayuwarmu ta yau, babu makawai sai al'umma ta samu jagoranci wajen yadda za a yi kyakkyawan amfani da waɗannan kafofi tare da samun hanyoyin daƙushe munanan tasiri da suke jawowa a rayuwarmu ta yau sakamakon amfani da waɗannan sababbin kafofin.
.
A burina na zaburar da malumanmu don mai da hankali a wannan muhimmin fage, na ga ya dace da na wallafa wannan É—an littafi a matsayin hanyar da zai taimaka wajen jan hankalin manyan malumanmu da su samar da litattafai da za su wayar da kan al'umma a wannan fage tare da shimfiÉ—a musu hanyoyin da za su mori amfani da waÉ—annan al'amri sakaka ba tare da jagorancin addini ba, ba zai haifarwa al'ummarmu É—a mai ido ba.
.
Wannan littafi ya yi tsokaci ne a kan muhimmancin sadarwa a tsakanin mutane, ɓullowar kafofin zamani na sadarwa da sada zumunta, alfanunsu da illolinsu. Sannan kuma ya taɓo yadda ya kamata al'ummar musulmi su yi amfani da waɗannan kafofin don cin moriyar fasahar lokaci da taɓewa bisa rqshin kyakkyawan amfami da sababbin sadarwa na zamani (social media)
.
Ina fata abun da littafin ya ƙunsa zai kasance mai amfani ga al'ummarmu, musamman ma matasa, sannan kuma a ɗaya ɓangaren ya zama sanadin zaburar da masana wajen cikakken nazarin ƙalubalen da ke tattare da amfani da kafofin sadarwa da sada zumunta a tsakanin al'umma, don shata mana kyakkyawar makoma a fage mai cike da sarƙaƙiya.
.
Ina roƙon Allah ya taimake mu, ya ba mu dacewa a duniya da lahira, amin. Ina matuƙar godiya ga malaman da suka duba min wannan littafi, Allah ya saka musu da dubun alheri, amin.
.
Aliyu Muhammad Sa'id Gamawa
P. O. Box 15 Gamawa.
Bauchi State, Nigeria.
aliyugamawa@gmail.com
Post a Comment (0)