KA KIYAYI HARSHEN KA

KA KIYAYI HARSHEN KA.


"A jikin harshenka akwai wata mummunar guba, wacce hatta kai kanka ma yana iya illata ka da ita balle waninka, matuƙar baza ka dinga kyautata furucinka da shi ba, kuma baza ka ke tsaftace zanceka da shi ba, to haƙiƙa zai jefa ka a cikin halaka a ranar ƙiyamah, domin lallai haƙiƙa tabbas shi harshe ana kifa fuskokin ma'abotansa kuma a jasu a ƙasa a ranar ƙiyamah, sune waɗanda basa kiyaye harshensu a yayin furta magana"
-
"Yana da matuƙar muhimmanci ka dinga tsaftace abinda bakinka zai dinga furtawa a koda yaushe tun gabanin furtawa ɗin"
-
"Magabata na ƙwarai sukan iya ƙididdige abin da harsunansu suke faɗa a duk rana sabida ƙarancin maganarsu wacce bata karantarwa ba, sukan yi matuƙar sarƙafe harasansu da kange shi daga yawan surutu marasa amfani"
-

Post a Comment (0)