RAKA'ATAL FAJR



_*RAKA'ATAL FAJR*_

_Daga Zauren_
_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_

_Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta (ﷺ) da iyalinsa, da sahabbansa da sauran wadanda suka bi shi da kyautatawa har zuwa ranar Alqiyamah._

_Na yi wannan rubutu ne a kan sallar raka'atal fajr don in tunatar da 'yan uwa alkhairin da ke cikinta. Allah Ya sa mu amfana da abin da za mu karanta._
....
....
_*Raka'atal Fajr* ko *Raka'atainil fajr* sallah ce da ake yi yayin da *alfijir* ya fito kafin sallar Subhi, sallah ce ta nafila wacce take dauke da raka'o'i guda biyu kacal amma kuma tana dauke da falala mai tarin yawa._

*Falalar Raka'atal Fijr:*

_Manzon Allah (ﷺ) ya ce:_

*”ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها“*

_Ma'ana: *“Raka'atal fajr ta fi alkhairin duniya da abin da ke cikinta”* (Muslim)_

_'Yan uwa! Raka'atal fajr sallah ce mai dauke da *raka'o'i* guda *biyu* kacal, wadda in shaa Allah mutum ba zai dauki sama da minti goma *(10 minutes)* yana yinta, amma kuma falalar alkhairin da ke cikinta ya fi *duniya* dukanta da abin da ke cikinta._

*Wasu Surori ake karantawa a Sallar Raka'atal fajr?*

_Idan mutum zai yi sallar raka'atal fajr a gida, to *Fatiha* kawai ze karanta banda surah. Amma idan a masallacine, to zai karanta *Suratul Kafirun* a raka'ar farko, da *Suratul Ikhlas* a raka'a ta biyu. Kamar yadda ya tabbata a wannan hadisin;_

_عن أبي هريرة: ((أن النبي ﷺ قرأ في ركعتي الفجر: *{قُلْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلْكَٰفِرُونَ}* [الكافرون: ١] و *{قُلْ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ}* [الإخلاص: ١]. رواه مسلم._

_Daga Abu Huraira: (Lallai Annabi (ﷺ) ya karanta a cikin raka'atal fajr: *{Qul yã ayyuhal kãfiruun}*[kãfiruun: 1] da *{Qul huwal Lahu ahad}* [Al-Ikhlas: 1). Daga Muslim._

_Wadannan sune surorin da ake karantawa a cikin raka'o'i biyun alfijir._

_Mu daure mu lizimci Wadannan raka'o'i don dacewa da falalar da ke cikinsu._

_Minti goma ya yi yawa ka kammala amma ladar ba ta misaltuwa. Allah Ya sada mu da alkhairan dake cikin wannan rana._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_

.
.
Zan dakata a nan, za mu ci gaba in shaa Allah. 

_Daga kaninku_

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh

4 Comments

Post a Comment