HUKUNCIN BIN MAI GAGGAWA ACIKIN SALLAH



HUKUNCIN BIN MAI GAGGAWA ACIKIN SALLAH
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum warahmatullah, dafatan Mlm yatashi lpy, tambayata shine Malam nice nake bin mijina sallah lokaci lokaci haka, to yana sauri dayawa kafin nagama addu'a da akeyi na cikin sujud da ruku'u yadago haka kafin nagama tahiya, ya hukuncin sallah na sannan inason sanin abubuwanda yakamata mutum yadinga karantawa indan yana bin liman sallah.
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.

Baiwar Allah, barakallahu fiki wa ahliki. Ki fara da yi mashi nasiha ta hanyar da ta dace, dangane da abin da Annabi yace da wani Sahabi da ya munana sallar shi saboda gaggawa da rashin cika rukunnan ta. Annabi yace da shi bai yi sallah ba, ya sake sallah, ma'ana Allah bai karɓa ba
Idan ya gyara shi ke nan, kina da sallah yana da sallah, amma idan ya ƙi ya ɗauki nasihar ki, kamar yadda Manzo yace, wanda duk ya limanci mutane ya dace, a ƙarshen hadisin yake cewa, wanda ya tauye wani abu daga haka, ku (mamu) laifi na kan shi, ku kuma ba laifi a kan su.
ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﻋَﻠِﻲٍّ ﺍﻟْﻬَﻤْﺪَﺍﻧِﻲِّ ﻗَﺎﻝَ : ﺳَﻤِﻌْﺖُ ﻋُﻘْﺒَﺔَ ﺑْﻦَ ﻋَﺎﻣِﺮٍ ﻳَﻘُﻮﻝُ ﺳَﻤِﻌْﺖُ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻳَﻘُﻮﻝُ : )) ﻣَﻦْ ﺃَﻡَّ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﻓَﺄَﺻَﺎﺏَ ﺍﻟْﻮَﻗْﺖَ ﻓَﻠَﻪُ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻭَﻣَﻦِ ﺍﻧْﺘَﻘَﺺَ ﻣِﻦْ ﺫَﻟِﻚَ ﺷَﻴْﺌًﺎ ﻓَﻌَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﻻَ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢْ )).
Duba da wannan hadisin, ke kina da sallar ki, shi kuma baya da sallah. Don haka kar ki samu dawuwa.

Wallahu ta'aala a'lam.

Amsawa
Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Kuturawa Yan'uwanku wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana.

1 Comments

Post a Comment