HUKUNCIN JININ 'BARI (MISCARRIAGE) :

HUKUNCIN JININ 'BARI (MISCARRIAGE) :

TAMBAYA TA 2997
*******************
Assalamu Alaikum malam barka da dare malam Don Allah tambaya ce Dani? Malam Don Allah menene hukuncin azumina matar da awatan Ramadan tayi barin cikin da baifi wata daya ba sannan jini yaki tsaya mata natsahon sati uku malam tanbayata itace Yaya zata bar azuminne har saiyadauke? Nagode Allah ya saka da alheri.


AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Akwai sa'banin malamai game da irin wannan jinin. Amma dai maganar da tafi kusa da daidai ita ce: Idan mace ta barar da cikin da bai kai kwanaki 81 ba, to jinin da ya biyo bayan 'barin, ba jinin haihuwa bane. Hukuncinsa shine irin hukuncin jinin rashin lafiya, wato istihadha. 

Amma idan cikin da ta barar din yakai kwanaki 81 ko sama da haka, kuma akwai alamun halittar Dan Adam ajikin abun (wato kamar siffar hannu ko Qafafu ko fuska) to wannan za'a daukeshi amatsayin jinin haihuwa ne. 

Malamai sun ce mafi Qankantar kwanakin da jariri yake fara daukar siffar Dan Adam acikin mahaifiyarsa shine kwanaki 81. Kuma sun dogara ne da hadisin Abdullahi bn Mas'ud wanda ke cikin Sahihul Bukhariy, wanda yace :

Manzon Allah ﷺ ya bamu labari alhali shine Mai gaskiya abin Gaskatawa, cewa "HAKIKA ANA TATTARA HALITTAR DAYANKU NE ACIKIN CIKIN MAHAIFIYARSA, KWANA ARBA'IN YANA GAURAYAYYEN RUWA, SANNAN YA ZAMTO GUDAN JINI GWARGWADON HAKA, SANNAN YA ZAMTO TSOKA GWARGWADON HAKA....."

Wato yana fara juyewa zuwa tsoka ne bayan ya cika kwana 80 acikin cikin mahaifiyarsa. Don haka idan mace ta 'barar da gudan jini, ko kuma wani abinda babu alamar siffar dan adam atare dashi, to ba zata dena sallah ko azumi saboda wannan ba. Kuma mijinta zai iya saduwa da ita. 

Amma idan taga alamar siffar Bil Adama atare dashi, to zata dauki wannan jinin ne amatsayin jinin haihuwa. Zata dena sallah da azumi har sai ya dauke. Idan har ya haura kwanaki arba'in (ko sittin bisa mazhabin Malikiyyah) to sai tayi wanka taci gaba da ibadunta, jinin kuma ya zama na jinya kenan. 

DON QARIN BAYANI ADUBA :

ALMUGHNEE Na Hafiz Ibnu Qudamah Almaqdisiy (juzu'i na 1 shafi na 211.

MAJMU'UL FATAWA na Shaikh Ahmad Ibnu Taimiyyah Alharraniy (juzu'i na 22 shafi na 102).

WALLAHU A'ALAM. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (23/11/1443 23/06/2022).

4 Comments

Post a Comment