KU KIYAYE ABUBUWA SHIDA ZAKU SAMU ALJANNAH

KU KIYAYE ABUBUWA SHIDA ZAKU SAMU ALJANNAH


Sahabi Ubadata bin Samit Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, "Ku lamunce min abubuwa guda shida (zaku kiyayesu) Ni kuma zan lamunce muku shiga Aljannah, su ne kamar haka;
1. Idan zaku yi magana to ku faÉ—i gaskiya 
2. Idan kun yi alƙawari ku cika.
3. Idan an baku amana to ku cika (kada kuyi ha'inci).
4. Ku kiyaye al'auranku (kada ku aikata zina).
5. Ku rimtse idanunku (kada ku kalli alfasha da duk wani nau'i na haram).
6. Ku kame hannayen ku (kada ku zubar da jinin wani, ko ku dakeshi, ko ku kwace dukiyar sa bisa zalunci). 
صحيح ابن حبان ٢٧١

#Zaurenfisabilillah 

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)