MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN KISHIYATA

45. MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN KISHIYATA.


*_Tambaya:_*
Assalamu alaikum. Mun kasance mu biyu a wajen mijinmu, amma 'yar uwata ba ta iya gamsar dashi, to ko ranar girkinta ya kan shigo ya tara da ni da rana ko da daddare. Tambaya anan shine; malam shin hakan ya halatta? kuma idan na mishi magana ya daina zuwa ba ya ji, ba gidan mu É—aya ba, don Allah hukuncin hakan da mafita. 

*_Amsa:_*
Wa alaikum assalam. Ya wajaba ya nemi izininta, tunda hakkinta ne, in har ta sarayar ya halatta ya sadu da ke a kwananta, saboda lokacin da Nana Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi (S.A.W.) ya sake ta, ta É—auki kwananta ta bawa nana A'isha, kamar yadda Bukhari ya rawaito, hakan yasa Annabi (S.A.W.) yana yin kwana É—ai-É—ai a É—akunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana A'isha yana mata kwana
biyu, Saudat kuwa ba ya kwana da ita, saboda ta sarayar da hakkinta.

Ya wajaba mai gida ya guji dukkan abinda zai kawo matsala da fitintinu a tsakanin iyalansa, adalci yana tabbatar da zaman lafiya. Duk wadda yake da mata biyu, bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar Alkiyama É“angarensa É—aya a shanye.
_Allah ne mafi sani._

_*Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.*_
Post a Comment (0)