AL'UMMATA


AL'UMMATA

Al'ummata
Ku mu hankalta
Mu daina mita
Mu Ι—au nagarta
Da halin bauta

Bismillahi Allah da ya yo sammai
Shi ya yo bishiya har da fa su Ζ™assai
Shi ya yi duniya ya ce a bauta mai
Shi ya yi dolaye kana ya yi jarmai
Ya ibadallah ya kamata mu bauta mai

Allah 
Tsira da aminci wurinsa abin Ζ™auna
Manzo habibi Ι—aha abin Ζ™auna
Salati wurinsa Ι—a wajen Amina
Shugaban halittu Ι—aha abin sona
Ya ibadallah gare shi mu yi biyayya

Manzo

Ya ibadallah gunku na zo yau ni
Ga tunatarwa ga duk mai imani
Gare mu dukka ku har zuwa ni
Ku mu hankalta mu kama addini
In kuma muka Ζ™i za mu shige tasku

Wayyo

Mai jan kunne kun san dai bai son mu
Baya son mu ko ci gabanmu
Al'adarmu har addininmu
Duka bai son su har da abincinmu
To mu Ι—au Ι—amara don gyaran kan mu

Bayi

Maimakon haka nan sai muka Ι—au wasa
A tsakaninmu muna ta sa-in-sa
Wasu na talla wasu na shan barasa
Ana kashe mu kamar mun zama mussa
To ibadallah ya kamata mu hankalta

Ya fi

Wanda bai son mu shi fa muke Ζ™yama
Wanda ke son mu sam ba ma sonsa
Rana zafi inuwa na Ζ™una
Ga mu nan zaune muna ta hayyasa
To ibadallah ya dai kamata mu hankalta

Ya fi

Ku mu hankalta mu Ι—au halin nagarta
Mu daina mita mu koma yin bauta
Ku mu hankalta ku al'ummata
Ku mu Ι—au gyara maza duka har mata
In mukai hakan za ko mu rabauta

Bayi


Al'ummata
Ku mu hankalta
Mu daina mita
Mu Ι—au nagarta
Da halin bauta

✍🏻 Jamilu Abdulrahman 
        ( Haiman Raees)
Haimanraees@gmail.com

Post a Comment (0)