Sheikh Aliyu Said Gamawa ya Rubuta!
KANA SHIRIN BARIN DUNIYA?
Allah ya kaddarawa duk mai rai dandanan mutuwa, kuma aka boyewa kowa rana, lokaci, gari da sanadin mutuwar mu.
Kullum muna raguwa daidaya har a iso kaina, kai ma a iso kan ka. Duk mai tsoron mutuwa ko gudunta ya sani Allah ya hukunta kowa tabbas sai ta riskeshi.
Idan wani ya rigani sai in dunga jimamin yadda yasa tufa da kansa gashi ana tube masa don wanka, in ga jikin nan da ake wanka da yi masa ado an cusa shi a rami an bisne, naga 'yan uwa da masoya sun juyo sun bar mutum a cikin matsatstsen raminsa daga shi sai halin sa da aiyukan sa.
Kwana kadan sai naga an fara manta shi, masu kuka sun dawo dariya, masu hawaye sun goge suna cewa mi ya bari, yaya za'ayi da gidan sa, bayan watanni matar sa tayi adon neman wani mijin, 'ya 'yansa a fara kiran su marayu.
In macce ce ta rasu sai mijinta ayi ta matsa masa ya auro wata, zuriyar data bari su dawo hannun wata, dukiyar ta a raba, miji ya tare da amarya yana ta murna..
'Yan uwa mu sani kullum kara kusa muke da komawa ga Allah. Kuma tabbas anan duniya ake tanadin samun sauki da dadin lahira.
Hakika da aiyukan mu na gabobi, harshe da zuciya za'a yi mana hisabi.
Muji tsoron Allah, mu dinga inganta imanin mu ta hanyar tsammanin kullum ba zamu kai karshen wuni ba, in dare yayi muna kaddarawa ba zamu kai gobe ba. Ko in muna aiki mu dauka shine na karshe..
Allah yasa muyi karshe mai kyau, yasa mu dace duniya da lahira, Ameen ya hayyu ya qayyum.