IDAN NA KUSANCI MIJINA YANA ƘYAMATA, MENENE MAFITA?



43. IDAN NA KUSANCI MIJINA YANA ƘYAMATA, MENENE MAFITA?

Tambaya:
Assalamu alaikum Malam. Ni ce ina da miji, a duk lokacin da zan zo kusa dashi sai yace min barci yake ji, ai shari'a ta hana na dame shi, a haka zamu yi kusan wata ba abin da ya shiga tsakanina dashi. Allah taimaki Malam, menene mafita?

Amsa:
Wa alaikum assalam. Ki tambaye shi dalilin da yasa yake yin hakan, zai iya yiwuwa kin ɓata masa rai ko kuma akwai wata matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata lamura za su iya fitowa fili. Shari'a ba ta halattawa namiji ya ƙi saduwa da matarsa ba da gangan, saboda nau'i ne na cutarwa. Yana daga cikin manufofin aure katange ma'aurata daga kallon haram.
Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.
Post a Comment (0)