DUNIYAR MALAMAN ISLAMIYYA 01

DUNIYAR MALAMAN ISLAMIYYA 01
.


.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+2348167807912
.
.
Yau 29/ 11/ 1441 wanda yayi dai-dai da 20/ 07/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka! Jama'a wannan lekcar ce ta musamman wanda ainihin lekcar zai fito nan gaba da yardar Allah ta'ala, amma wannan zai zamo mukaddima ne kafin mu fara ainihin lekcar mai taken *DUNIYAR MALAMAN ISLAMIYYA*. Wannan lekcar zaiyi bayani akan yadda ake mu'amala da malaman islamiyya da kuma yadda wasu daga cikin malaman islamiyya suka lalace suka manta da amana ta ilimi. Nasan wasu zasuyi mamaki saboda na takaita lekcar zuwaga malaman islamiyya zallah, a'a karkuyi mamaki wannan lekca ce wanda sakonnin cikin lekcar tana magana ne akan duniyar malaman islamiyya baki daya musamman ma na Nigeria. Nasan wasu kuma zasuyita mamaki cewa dama malaman islamiyya sunada duniyar nasu ta musamman? A'a basuda duniyar tasu ta musamman duk suna cikin duniyar nan tamu ne wanda muke rayuwa aciki. Jama'a Idan baku manta ba a lekcar mu ta *DUNIYAR ALJANI DA SHAIDANI* munyi bayani akan me ake nufi da Duniyar kaza, kamar ince Duniyar Aljani da Shaidani duk munyi bayani a wannan lekcar, saboda haka idan nace *DUNIYAR MALAMAN ISLAMIYYA* tho ba wai ina nufin wata duniya daban ba, a'a wannan duniyar tamu ne suke rayuwa aciki. Idan nace *DUNIYAR MALAMAN DARIKA* tho ina nufin malaman darika gaba daya, hakama idan nace *DUNIYAR MALAMAN IZALA* tho ina nufin malaman izala baki daya. Tho amma sai nace *DUNIYAR MALAMAN ISLAMIYYA* tho anan zakuga ina magana ne akan duk wani malami wanda yasan yana koyarwa a makarantar islamiyya, indai har kai me koyarwa ne a islamiyya tho da kai wannan lekcar take magana, saboda haka ka bibiyi lekcar. Ina fatar an fahimta??_

_Jama'a suwaye malamai tukunan? Malamai sune:-_
*الذين يدلون على طاعةالله ويحذرون من اتباع الشيطان*
_Wato sune wadanda suke nuni gameda yiwa Allah biyayya kuma suke gargadi gameda bin shaidan. Kuma a wani hadisi Manzon Allah s.a.w ya fadamana cewa malamai sune magadan Annabawa. Ina fatar an fahimta?_ 

_Malaman islamiyya malamai ne da suke da daraja, kuma malamai ne da ya dace a girmama, a karrama, a mutunta, a taimaka. Malaman islamiyya sune ya dace a koyawa yara girmama su da daraja su. Amma abin takaici abin bakin ciki an mayar da malaman islamiyya kaskantattu marasa daraja sune abun wulakantawa. Subhanallah._

_A wannan duniyar nan tamu ta mutane anfi daukar malamin boko da daraja fiyeda malamin islamiyya, yau in akaga malamin boko da mota tho ba a damuwa, amma idan akaga malamin islamiyya da mota sai ya zama abun gulma da tuhuma. Jama'a hatta sabuwar riga in malamin islamiyya ya canza sai ya zama abun gulma. A yau an mayar da malaman islamiyya kaskantattu ba a koyawa yara girmama su, shiyasa zakuga idan yaro yayi laifi a makarantar islamiyya malami ya dukeshi, tsabar rashin kunya irin na uwa ko uba sai a tasa yaron a gaba suna kumfar baki sun kawo kara, ni na taba ganin malamin islamiyyar da aka kai karar sa wajen yan sanda. Jama'a wane irin wulakanci ne wannan? Amma idan yaro yayi laifi a makarantar boko akayi masa duka, tho iyayen yaran basa damuwa ballantana ma su kai kara. Hakane jama'a??_

_Mafi yawan malaman islamiyya suna koyarwa ne don samun lada domin basu fiya dogara da albashi da ake basu ba. A lekcar da nayi akan Makarantar Certificate nayi bayani cewa yanzu ba a dauki addini da muhimmanci ba balle a dauki me yiwa addini hidima da muhimmanci. Shiyasa zaka samu yaro dan masu kudi a makarantar islamiyya ba a biya masa kudin makaranta, kudin da basu wuce dubu biyu zuwa biyar ba basa biya sai sunga an takura musu. Amma na makarantar boko tun kafin a fara tambaya suke biya kuma a kalla suna biyan dubu ashirin zuwa dari biyu, ni na taba ganin wanda yake biyawa dansa a primary school kudin school fees har naira dubu dari biyar a term wallahi. Hakan ba laifi bane don anyi, amma tunda har kuna iya fitar da kudadde don yaranku su sami ilimi me kyau a makarantar Boko, tho meyesa a makaranta islamiyya bakwa iya biyawa yaranku kudin makarantar islamiyya??_

_Jama'a zamu dakata anan saboda banaso rubutun yayi yawa, ku kasa fahimci sakon da wannan lekcar ta kunsa. Sai mun sake haduwa a lekca ta gaba._
=
=
_Dan uwanku na yau da kullum a musulunci da Sunnah_
°
*_✍ABDULRASHEED IBN MUSA(ABU-MANAL)_*

°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)