KUNDIN MA'AURATA // 01
.
بسم الله الرØمن الرØيم
Namiji da mace a matsayin ma'aurata matsayinsu guda ne, kamar fukafukan tsuntsu, yadda zaman aure bai yuwuwa sai da su gaba daya, kamar yadda tsuntsu bai iya tashi da fuffuke guda, sai dai kuma Allah SW ya fifita namiji akan mace da abubuwa da dama, ciki har da dawainiyar da shi namijin kan dauka tun daga neman auren har rayuwar abadin-abadin, muslunci kuma ya kasa ayyukan da kowa zai yi, duk da cewa wani zai iya kama wa dayan a matsayin mataimaki, misali Namiji an san shi da kula da ayyukan waje ne, amma ba laifi in ya tsaya kan taimaka wa iyalinsa wurin wankin kwanoni da dafe-dafen abinci zuwa sharar cikin gida da ban daki.
.
Haka mace aka san ta da kula da yara zuwa aikace-aikacen da suka shafi cikin gida, amma ba laifi in tana wata sana'a ta kama wa maigidan don taimaka masa, masamman abubuwan da suka shafi yara, daga gida zuwa karatunsu, galibin wadannan abubuwan ba wajibi ba ne, amma akan yi su don sanyaya wa masoyi, da qara danqon zaman-takewa, kowa aka kyautata masa ya sani, koda kuwa ya furta a lafazance ko bai ce komai ba, amma qoqarin cewa mace da namiji daidai da daidai suke a komai, wannan yaudarar kai ce, Allah SW ya fadi qarara cewa maza su ne jagororin gida don abin dake kawunansu na hidindumu.
.
To amma kuma an sami wani hadisi wanda Annabi SAW yake ba wa wani sahabi amsa lokacin da ya tambaye shi wanda ya fi cancanta da ba shi kulawa a tsakankanin mahaifansa guda biyu, ya ce masa mahaifiyarsa, sai da ya kira sunanta sau 3 bai canza ba, kafin ya kira mahaifin a karo na 4, bisa wadannan dalilan nake ganin kowa yana da tasa gudummuwar da yake badawa, kuma ya san iyakarsa, qoqarin da ake samu na qetare haddi zuwa aikin wani, shi ne babban taho-mu-gaman da ake samu a cikin gida, wato lokacin da mace ta yi qoqarin karbe ragamar gidan, ko ta yi tunanin cewa matsayinta daya da na maigidan, ko shi ya nuna cewa ita ba kowa ba ce, ko an kawo ta ta yi masa bauta ne kawai ba tare da kula da wasu haqqoqinta ba.
.
ZAMAN AURE
Rayuwar zamantakewar aure takan fara ne da musayar qauna tausayi da tarairayar juna, a daidai wannan gabar dole ne mace ta fahimci bambancin gidan ubanta da nata na kanta, kafin ta yi aure komai yi mata ake yi, bayan ta yi kuwa komai ita za ta yi, ta gane cewa duk ayyukan gida wajibinta ne ba taimakon mijin take yi ba bare ta sa rai da zai gode mata ko ya saka mata, in ya yi to madalla, in bai yi ba dama ba binsa bashi take yi ba, haka shi ma mijin ya gane cewa duk abin da gida yake buqata a wuyansa yake, in ya kawo ya sauke nauyin da Allah SW ya daura masa, ba wai rufa wa matar asiri ya yi ba.
.
Idan ya kasance kowa yana qoqarin ba da haqqin da Allah SW ya dora masa daidai gwargwado, da wahala ka sami qananan rigingimun cikin gida bare har a kai ga saki ko kisa, a 'yan shekarunnan ne kawai muka fara jin namiji ya nakada wa matarsa dukan tsiya har ya kai ga an kwantar da ita a asibiti, wata kuma an cire mata haqori, wata mijin ya la'anta mata ido, su kuma matan muka tsinci wata ta yanke wa mijin mazakutarsa, wata ta nemi ransa da takin zamani, wata ta yi masa yankar rago, wata ta soka wa nata wuqa, ga dai abubuwannan daban-daban, galibin wadannan matsalolin in ka saurara sai ka ji ba su kai matsayin da za a dauki wadannan manyan matakan ba, abin takaicin kuma sai an zartar da abin da ake so sannan a zo a fara kuka, wadannan da wasunsu su za mu karanta cikin yardar Allah SW.
.
DAIDAITUWAR MACE DA NAMIJI
Duk lokacin da aka tashi maganar aure a Hausance za ka ji cewa namiji ne ya sa dukiyarsa, ko matsayinsa na dangane da ilimi ko aikin gwamnati ya nema, ya kuma biya sadaki ya aura, ya dauki duk nauyin da ya dace na ci da ciyarwa da tufatantarwa, kana ya dauko ta daga gidan mahaifanta da suka qosa ta sami gidanta, ya kawo ta, ko wannan ya isa ya dauki matsayin jagora koda kuwa dukansu matafiya ne, kenan ba sanannen abu ba ne a ce mace ta samo mijin da take so ta neme shi, a wasu matattarar ma furta cewa ita ta fara nuna tana son sa zubar da daraja ne gami da wulaqanta kai, duk kuma hidindumun da suka shafi daura aure duk manemin zai dauka, koda kuwa goron daura aure ne, to bare motocin daukar amarya, da wannan za mu san cewa shi ne a gaba, ko ba komai gidansa ne, shi ne maigida.
.
Mace kuwa duk abin da za a shugo da shi aikinta ne ta sarrafa shi ta hanyar da ta dace, tare da bin dokokin da maigidan nata ya shimfida don neman zaman lafiya, kenan ko dukansu uwaye ne, mijin shi ne shuga, ita kuma mataimakiya, za ta iya yin aikinsa a lokacin da ba yanan ko a halin da shi ya yarda da hakan, shi ma zai iya yin nata bisa tausasawa ko ya dauko wanda zai taimaka mata tare da samun sararin yin hakan, amma wani abu mai matuqar mahimmanci shi ne fahimtar sabanin dake tsakanin namiji da mace a halitta da dabi'a, muslunci ya lura da wannan sosai wajen raba ayyukan kowa a cikin gida, in muka kiyaye wannan to za mu iya taimaka wa juna gami da yi musu hanzari a wasu qananan abubuwa da suka gaza a tsakaninsu.
.
Namiji ya dace ya san cewa mace na da buqatar a lallaba ta ta kowane hali, komai girmanta ko qanqanta, duk da cewa yana da dan kaushi da son girma, da rashin saurin tasirantuwa da matsalolin ko amsar abin da aka kawo masa ba tare da ya yi tunani ba, yakan yi aiki da hankali sosai wajen yanke hukunci, mace kuma mai raino ce kuma mai gadin gida da yaranta, takan yi wannan aikin cikin sauqi ba tare da hayaniya ba, in za ka fahimci wannan to ka lura lokacin da yara suke fada a lokacin da ubansu yake gida, ka qiyasta yadda yake maganin matsalar da yadda ita uwarsu take yanke hukunci, kenan dole mu yadda da wani bambanci da Allah SW ya qirqira a tsakanin wadannan halittu guda biyu, koda kuwa mun yi ta musayar yawu da daga murya kan cewa duk daya suke saboda qarancin masaniyarmu da addini.
*Muhimmin sako*
*A gafarcemu da Rashin bude group dan yin gaisuwar sallah hakan y faru saboda uzuri da yayi yawa a gafarcemu Allah y maimaita mana ya hadamu a Aljannah*
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248