'YAN MAƊIGO

Rayuwa mai yayi, rayuwa mai abin gani mai kuma abin fada, rayuwa mai kyara tarbiya mai kuma bata ta. Babban abu mafi muni shine rugujewar tarbiyar ‘ya mace, don tarbiyan mace daya al’uma dubu kan tarbiyantu, matsalar, idan tarbiyan mai kyaune, dubu zasu yi kyau haka idan mummunace dubu sun lalace.

 


Madigo wato ‘Lesbian’ tsakanin mata wani sabon salon lalacewan ‘ya mace ne da a yau ke dada tashe a cikin al’umma. Madigo na nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin macce da mace ta amfani da tsiraicinsu ko cikon halittun matancinsu don jin dadi ko kau da sha’awar junansu. Ayau bincike ya nuna akan samu yaran mata dag shekaru takwas zuwa sama na cikin harkar.

 

Ga siffofin mata masu yin madigo ‘lesbians'

 

Tsanan da namiji, rashin sha’awarsa da rashin sha’war yin aure.
Suna nuna wa juna tsananin soyayya (macce da macce) da nuna damuwa idan basu hadu ba.
Suna nuna tsananin kishi yayin da abokiyar harkarsu ta fara mu’amala da wata.
Suna da kalaman gane juna, misalai, ‘muna tare ne?’ ‘kina harkane?’ ‘kin tayarmin da tsumi’ ‘za ki yi dadin harka’.
Suna son yin amfani da kwayoyi dake tunkudo cikon halittarsu, kamar kirjinsu ko mazauninsu.
Wasu sukan sanya zube a yatsunsu na kafa.
Wasu daga cikin abubuwa dake jefa mata harkar madigo lesbianism:

 

Makarantar kwana ta mata, yakan fara faruwane yayin da mace ta kai matakin sha’awar da-namiji, takuma sami kawaye masu karancin tarbiya.
Amfani da manyan wayoyi dake sadasu da fina-finan basa da kawaye masu madigo
Takurawa mace da kuma hanata aure a lokacin da take kishin ruwan da-namiji
Macen data taba sanin namiji ta kuma shiga takura na tsaro daga iyaye ko magabata.
Karancin ilimin na iyaye da rashin sanin hakkokin ‘ya’yansu akansu.
Zama da mace mai yin madiko ‘lesbian’.
Kau da kai daga sakamakon lahira
Shahara a munafurci da aikata sabo
Gudun daukan cikin shege
Don a yarda ita kamilace.


Illolin madido ‘lesbian’:

 

Tsanan da-namiji da rashin sha’awarsa
Masu madigo kan bi juna gidan mazajensu
Yin madigo kan haifar da masifu da bala’i
Wadanda suka yi nisa, idan sun yi aure mazajensu basa gamsar dasu
Basu damu su yi abin da mazajensu zasu gamsu dasu waje jima’I ba
Ba su cika son aihuwa ba.
Basa jimawa agidan miji
 

Akwai bukatan iyaye su farga, musamman iyaye mata sanin asalin kawaye dake mu’amala da ‘yarsu.

ALLAH YA KARE MANA ZURI’ARMU

1- Ki Nisanci Duk Wata Kawa Da Zata Dinga Bayyana Miki Tsaraicinta.
2- Kada Ki Yarda Kawarki Ta Yabaki Ta Fuskar Sha'awa.
3- Ki Guji Kawar Da Zata Dinga Rungume Ki Da Nufin Wasa.
4- Ki Tsoraci Kawar Da Zata Dinga Kunna Miki Fina-Finan 'Yan Madigo (Lesbian).
5- Kada Ki Yarda Kawarki Ta Kama Hannunki Na Tsawon Lokaci Ta Jima Tana Shafa Miki Hannu, Da Sannu Zata Kai Ga Mabudin Sha'awa Shine Ta Fara Shafa Miki Kirjinki.
6- Ki Nisanci Kawar Da Zata Dinga Yawan Shafa Gashin Kanki.
7- Ki Kauracewa Kawar Da Za ta dinga Yawan Kwanciya Ajikinki Batare da Wani Dalili Ba.
8- Ki Kyamaci Kawar Da Akodayaushe Zata Dinga Son Ta dinga Ganin Jikin ki, Kamar Kirjin Ki Da Bayan Ki Zuwa Kasan Marar ki.
9- Ki Rabu Da Kawar Da Za Ta Dinga Yawan Yi Miki Kyaututtuka Masu Tsada Ba Bisa Dalili Ba.

10- Ki Bar Kawar Da Take Yawan Jan Ki Zuwa Gidan Kawayenta Wa'yanda Bakisan Su Ba Kuma Basu Da Mazaje Koma Suna Da Mazajen, Amma Wa'yanda Ki Ka Ga Suna Yawan Kulewa Cikin Uwar Daka Ko Suke Yawan Tafawa Suna Rungumar Juna, Ko Kwanciya Akan Cinyar Juna Ko Suke Yawan Cire Tufafinsu Agaban Juna Ko Wanka Tare.
11- Ki Kyamaci Kawar Da Bata Da Hira Sai Hirar Mace 'Yar Uwar ta.
12- Ki Guji Kawar Da Ba Ta Son Yawan Mu'amala Da Maza Amatsayin Samari Ko Masoya, Amma Ta fi Mu'amala Da Mace 'Yar Uwarta Matuka Ainun.

13- Ki Kauracewa Kawar Da Take Da Sha'awar Kallon Fina-Finan Batsa Musamman Irin Na Mace Da Mace (Lesbian).
14- Ki Fita Sha'anin Kawar Da Ake Yada Jita-Jitan Tana Madigo (Lesbian).
15- Ki Rabu Da Kawar Da Take Mu'amala Da Kawaye Masu Madigo (Lesbian) Koda Ita Ba ta Yi Domin Kallon Mai Yi Akeyi Mata Kema Haka Za'a Yi Miki Kallo.

16- Ki Yakice Kawar Da Take Zaman Kanta Agidan Da Ta Kama Take Haya Kuma Mata Ke Taruwa A Gidanta.

17- Ki Fita Sha'anin Kawar Da Ba Ta Jin Kunyar Cewa Aga-Aga, Na Kirji Ko Baya Ko Kasan Marar Juna.
18- Ki Hakura Da Kawar Da 'Yan Madigo Ke Burgeta Koda Ita Ba Ta yi.
19- Ki Kyamaci Kawar Da Take Yawan Yabon Surorin Jikinki Irin Kirjinki Da Mararki Da Bayanki.

20- Kiyi Tir Ki Kuma Guji Tareda Kyamatar Kawar Da Kuna Haduwa Maimakon Tamiko Miki Hannu Kuyi Musabiha Sai Dai Takai Hannu Ta Daki Bayanki (Mazaunanki) Ko Ta Dan Shafa
Kirjinki.

Idan Siffar Kawarki Ya Burgeki Sai Kice "Masha Allah".

Ku Isar Da Wannan Sakon Ga Mata, Don Tseratar Da Su Daga Wuta.

Allah Yasa Mu Dace, Amin.

A makon da ya gabata mun fara tabo batun bala’in da wasu mata ke jefa kansu a ciki ta dibi’ar madigo inda muka yi shimfida kan masifun da abin ke jawowa da kuma yadda ake bata wa iyaye yara ta hanyar jefa su a muguwar dabi’ar bayan sun ba su kyakkyawar tarbiyya. A wannan makon ma har yanzu dai muna kan maganar ta mata ‘yan madigo. Hakika duk wacce ta samu kanta cikin irin wannan jarabawa ta madigo to tana cikin fitinar rayuwa, ita kanta ba wai don tana jin dadin samun kanta a ciki ba ne, domin da yawansu sun san wannan abu ba abu ne me kyau ba ta kowacce fuska. Yana da kyau iyaye mu kula da rayuwar yaranmu mata don guje wa fadawa ire-iren wannan dabi’ar.

 

A duk lokacin da uwa ta fahimci yarinyar ta tana da kawa da suke yawan ziyartar juna, to ta yi kokari ta yi bincike sosai. Ko ta gan ta da sabon wani abu da ta san ba ita ta saya mata ba ta binciket a inda ta samo, saboda wacce duk ke son rinjayar yarinyarta to tana iya mata kyauta ta bajinta. Alamomi Da Ake Gane Mace ‘Yar Madigo: Akwai alamomi masu tarin yawa wanda ake gani da ma wanda sai su kadai suke gane kansu. Kadan daga cikin wanda muke gani a zahiri sun hada da :

1. Suna da son yin kyauta ta bajinta ga mata musamman wadanda suka gani suna so.

2: Suna da mugun son yin dinkin riga matsattse me bayyana nononsu.

3: Idan sun hadu da wacce ta yi musu sun dinga yi ma ta farin ido wurin yi mata magana kenan don son jawo ra’ayinta.

4: Suna da son yabawa structure (kyan diri) na mace musamman wacce suke son jan ra’ayinta.

5: Sun fi koda kyau na mace fiye da namiji

6: Suna da mummunan kishi

7: Ba su damu da yin mu’amala da maza ba, kullum sun fi son su rabi mace cikin nuna sha’awa.

8: Suna da son kyalli da tsabta ta fitar hankali.

9: Suna da son yin mu’amala da kalolin turaruka.

10: Suna son saka sarka a kakarsu da zobe a yatsar kafar, duk da yanzu kusan an mayar da yin hakan gaye amma nasu na musamman ne.

Wadannan su ne kadan daga cikin alamomin da za a iya gane ‘yan madigo da su, amma ba su kenan ba. Kamar yadda na fadi a sama, akwai wasu alamomin da sai su da ke cikin muguwar dabi’ar ke iya ganewa ko kuma idan an yi la’akari da abubuwan da suke aikatawa da zarar sun hadu a tsakaninsu.

Iyaye sai mu kula a duk lokacin da muka ga wata alama makamanciyar wadannan ga yaranmu ko wacce ke mu’amala da yaranmu mata sai mu yi kokari mu yi wa tufkar hanci. A karshe wadanda suka samu kansu cikin wannan ibtila’i ta madigo muna yi musu addu’a da fatan nan gaba Ubangiji ya yaye musu ya raba su da ita, Allah ya shirya mu, ya tsare mu da sharrin mutanen zamanin namu, amin.


Post a Comment (0)