TAƁARGAZARSU GA ALI (RA)

TAƁARGAZARSU GA ALI (RA) 


A cikin Ζ™oΖ™arinsu na Ι“ata sunan shugabannin Musulunci da siffanta su da siffar marasa mutunci, malaman Shi’a suna dangana maganganu masu yawa ga Sarkin Musulmi Ali binu Abi Ɗalib, Allah ya Ζ™ara masa yarda, irin maganganun da ba mai furta su sai wanda ya kai matuΖ™a a rashin mutunci. Babban malaminsu mai suna Muhammad BaΖ™ir Almajalisi ya ruwaito cewa: Wata mace ta miΖ™e a cikin masallaci, alhalin Sayyidina Ali yana yin huΙ—uba, sai ta ce, “Ya kai makashin masoya!” Wai sai Sayyidina Ali ya dube ta, ya ce: “Ya ke mara kunya, ya ballagaza. Ya wacce ba ta haila kamar yadda mata ke haila. Ya wacce a kan abin naninta akwai wani abu da ya burtso, yana reto.” *[Duba Biharul Anwari na Muhammad BaΖ™ir Almajalisi, bugun Ihiya’ut Turathi, Bairut, 1403, mujalladi na 41, shafi na 293].* “ABINNANI,” wannan fassarata ce, amma shi mai ruwayar ya yi amfani da wata kalmar Larabci da take nufin FARJI, wacce idan da za mu fassara ta zuwa Hausa to da sai dai mu koma ga tsohuwar Hausa ta Maguzawa mu nemo kalmar.  

Saboda Allah, ya Ι—an uwa mai karatu, tana yiwuwa Ali binu Abi Ɗalib, Allah ya Ζ™ara masa yarda, ya furta waΙ—annan kalmomi, alhali yana kan mimbari yana huΙ—uba a masallaci? Kuma idan ya yi nufin ladabtar da wannan matar ne, ko mayar mata da martani, babu wasu kalmomin da suka fi dacewa da matsayinsa na Sahabi, kuma Ζ™anin Annabi (SAW), wanda ya taso aka raine shi a gidan Annabta? Babu shakka wannan Ζ™oΖ™arin Ι“ata sunan Ali ne, da ma sauran Ahalul Baiti, da Ζ΄an Shi’a suke yi, kuma a lokaci guda suna fakewa (suna yin TaΖ™iyya) da cewa wai su masu Ζ™aunar su ne. 

Har yau, akwai wani labari da Ζ΄an Shi’a suke bayarwa cewa, wai wata rana wata mace ta yi wa wani mutum Ζ™azafi, sai ta Ι—auki ruwan Ζ™wai farin, ta zuba shi a tsakanin Ζ™afafunta, ta ce wai ya yi lalata da ita, kuma wannan maniyyinsa ne. Wai sai Ali binu Abi Ɗalib (RA) ya tashi, ya duba tsakanin Ζ™afafunta, ya ce Ζ™arya take yi, wannan ba maniyyi ba ne!! *[Duba Biharul Anwari na Majalisi, mujalladi na 4, shafi na 303]* .  

Mai karatu, sai ka duba wannan magana da idanun basira. Ta Ζ™aΖ™a Ali zai duba tsakanin Ζ™afafun mace muharrama don kawai ya tabbatar da Ζ™arya ko gaskiyarta?! Shin duka garin ba wata mace wacce za’a sa ta yi wannan aikin? Shin wannan ba Ζ™oΖ™arin zubar da mutuncin Sarkin Musulmi Ali ba ne?     

*TaΙ“argazarsu Ga Nana FaΙ—ima (RA)*
Malaman Shi’a sun siffanta Nana FaΙ—ima, Allah ya Ζ™ara mata yarda, da siffofi waΙ—anda suke nuna matuΖ™ar suka da zubar da girma. A nan ma, za mu taΖ™aita saboda munin waΙ—annan siffofin.  

A dangane da gadonta da suka ce wai Khalifa Abubakar SiddiΖ™ ya hana ta, kuma wai Umar ya Ι—aure masa gindi a kan haka, suna ruwaito yadda ita FaΙ—ima Ι—in ta kai gwauro ta kai mari don neman gadon nata. Suka ce, “FaΙ—ima(AS) ta iske Abubakar da Umar a masallaci, ta yi musu maganar gadonta na gonar Fadak, inda ta yi faΙ—a da su, ta yi kururuwa, mutane suka taru, kuma ta kama wuyan Umar ta jawo shi zuwa gare ta.” *[Duba Kitab Salim binu Ƙais na Salim binu Ƙais Alhilali, bugun Mu’assasatul Bi’itha, Bairut, ba tarihi, shafi na 253].* 

Mai karatu ya dubi yadda wannan ruwaya ta siffanta FaΙ—ima:  matar aure, Musulma, ta iske mazaje, abokan ubanta (kuma surukansa), a bainar jama’a, ta yi faΙ—a da su a kan gona, har ta ci kwalar Ι—ayansu!! Shin idan ma wannan gadon ya dame ta, ba ta da miji, ko wani Ι—an uwa, da zai karΙ“o mata haΖ™Ζ™inta? Ai ba FaΙ—ima ba, wacce take Balarabiya, BaΖ™uraishiya, Bahashima, kuma Ζ΄ar Manzon Allah(SAW), ko wata Ζ΄ar Fulani Bakanuwa, ba za ta aikata wannan rashin mutuncin ba. Amma abin mamaki shi ne, Ζ΄an Shi’a sun yarda da wannan ruwaya, kuma suna kattaba ta a cikin littafansu!!
Irin waΙ—an nan maganganu na Ι“atanci da Ζ΄an Shi’a suke dangana wa Ahalul Baiti suna da yawa ainun a cikin littafansu. A nan, mun kawo Ι—an misali ne kawai don mu tabbatar wa da mai karatu cewa da’awar Ζ™aunar iyalin gidan Manzon Allah(SAW) da Shi’awa suke yi munafurci ne kawai da yaudara da TaΖ™iyya!!


*- JERIN LITTAFAN SHI’A NA 3: "AΖ™idar TaΖ™iyya a wajen Ζ³an Shi’a" - na Prof. Umar LabΙ—o*

*✍ AnnasihaTv*

*- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuΙ“e mu kamar haka;*

*Call/WhatsApp:* 08142286718

*Twitter:* https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)