BA TA SAN MIJINTA YA RASU BA SAI BAYAN SHEKARU BIYU, ZA TA YI TAKABA??

BA TA SAN MIJINTA YA RASU BA SAI BAYAN SHEKARU BIYU, ZA TA YI TAKABA??



Tamabaya

Assalamu alaykum, Dr mutum ne yarasu da shekara biyu, sannan matarsa ta sami Labarin rasuwar sa, kuma ba'a raba auren ba, shin zatayi takaba daga sanda ta sami Labarin ne.? Allah yasaka wa Dr da aljannah

Amsa
Wa alaikum assalam, In har ba ta sani ba sai wannan lokacin da ka ambata, to babu komai akanta, saboda Iddar takaba tana farawa ne daga lokacin da mamaci ya rasu.

Wannan ya sa macen da mijinta ya rasu ba ta sani ba sai bayan wata hudu da kwana goma ba za ta yi takaba ba, tun da lokacinta ya wuce.

Don neman Karin bayani duba Fatawar Ibnu Bazz mai lamba ta: 823, wacce ya yi ta a ranar: 7/5/1389 H.

Allah ne mafi sani
Amsawa...

Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

12/05/2017

Miftahul ilmi 
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)