SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {01}

SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {01}




بسم الله الحمدلله والصلاة والسلام على رسول الله وعلى آله وصحبه ومن تبعهم بإحسان إلى يوم الدين.

Na fara rubutun nan mai suna : SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI? da sunan Allah maɗaukaki Ubangijin mutane da Aljanu, mai iko akan kowa da komai, mai bayar da lafiya ga wanda yaso kuma ya karbe lafiya ga wanda yaso, mamallakin rayuwa da mutuwa, ina rokonKA da sunayenka tsarkaka na ALHAYYU ALQAYYUM kasanyawa rubutun nan albarka kuma kasa ya zamto mai amfani ne ga al'ummar Musulmai da musulunci, kuma ka daidaita min alqalami na wajan rubuta abinda kake so kuma ka yarda da shi sannan ka tsare Ni daga rubuta duk wani abinda kake kyama kuma kake fushi da shi. 

Tambayar da mutu ne da dama ke yi itace:

1- Shin Jinnu za su iya rabuwa da mutum kuwa?

2- Shin ana warkewa daga cutar Aljanu kuwa?
 Da sauransu.....

 Kasantuwar da dama sai kaga wasu sun dade da jinnu a jikinsu, ana ta yin magungunan ana ta yin ruqyar amma kuma sai kaga har yanzu bai bar jikinsu ba kuma basu warke ba, wasu ma sai kaga gwamma jiya da yau.

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji amsar yadda al'amarin yake amma a takaice.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)