*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
*ALWALA*
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*FUTOWA TA 👇*
*(22)*
*BARIN YIN BISIMILLAH YA YIN ALWALA*
Yana daga cikin kusakurai da muke yi shine sabawa maganar manzan Allah (saw) da yake cewa "Babu sallah ga wanda baiyi Alwala ba haka zalika babu Alwala ga wanda bai ambaci sunan Allah ba".
Saboda haka Imamush shaukani yake cewa ibn sayyidin nas yana cewa acikin sharhin tirmizi : wannan hadisin yana nuna wajibcin yin bisimillah ya yin Alwala, Mazahabar Hanabila sun tafi akan cewa wajibine yin bisimillah ya yin Alwala, Amma Malikiyya da shafi'iyya da Hanafiyya sun tafi akan cewa sunnah ne yin bisimillah, suka qara da cewa barin yin bisimillah ba ya nuna mutum bashi da Alwala sai dai rashin kyautatuwarta kamar hadisin da manzan Allah saw yake cewa babu "sallah ga makocin masallaci sai acikin masallaci " hakan ba yana nuna bashi da sallah ba kwata kwata sai dai rashin kyautatuwarta kuma suka qara da hadisin da yake cewa "Ambaton Allah acikin zuciyar mumini yake ya furta ko bai furta ba " haka zalika imamul baihaqi shima ya tafi akan cewa ba wajibine yin bisimillah ba, saboda hadisin da yake cewa "Sallar dayanku bata cika har sai ya yi cikakkiyar Alwala kamar yadda Allah ya umarta " imamun nawawi yana cewa a wannan mas'alar zamu iya kafa hujja da hadisin Abi huraira da yake cewa "Duk kan wani Al'amari da ba a ambaci sunnan Allah acikinsaba to yan kakkene ".
Ataqaice anso mutum ya yi bisimillah kafin fara Alwala domin da cewa da sunnar farin jakada (saw).
*ALLAH SHINE MASANI*
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*MU HADU A FUTOWA TA 23*
*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏