SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {05}


SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {05}

10- Yarda da duk maganar da ta fito daga bakin Jinnun ( musamman a lokacin da ake yin ruqya) ko a rika aiwatar da umarnin da Aljanun ke bayarwa akan mqra lafiyar ko kan wasu dabam, Lallaikam hakan yana kara tabbatar musu da cewa sun samu karbuwa kuma yakara musu izzah da sarauta, kuma su rika ganin ai fa su yanzu sunga wurin zama na dindindin. Allah yakara tsare mana imaninmu.

Duk wadan nan bayanan daga na 1 har na 10, suna daga cikin abubuwan da suke kara kusanto kuma su tabbatar da jinnu a jikin mutum kuma su hana su fita saboda jin dadin da suke ji da kuma kulawar da sukaga ana nuna musu, sai suyi ta wahalar da mara lafiyar kuma su wahalar da masu jinyarsa wajan da kashe kudadensu domin samarwa dan uwansu magani.

Maganar gaskiya cutar Jinnu ba kamar cutar da ka saba da ita bace a dabi'ance, kuma yanayin magance cutar ma ba kamar yadda ake yiwa sauran cututtukan bane, kuma jinyarta ma ya sha bambam da jinyar sauran cututtuka saboda ita dabam take. To tunda har lamarin ya kasance haka mun fahimci ba daya suke ba ya kamata mu rika baiwa masana irin wadannan cututtukan hadin kai domin samun mafita da kuma dacewa cikin Ƙarfin Allah da buwayarSA da Kuma ikonSA, amma hadin kan nan ba ya yiwuwa sai in har an fahimci masu maganin suna bin tsarin da Nassi ya karantar da kuma koyarwar magabata na kwarai don gujewa dibar kara da kiyashi, ba masu tafiya akan tsarin bokanci da surkulle ba .

Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)