*HUKUNCIN MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA*
Fatawar Mata fitowa ta 1
*TAMBAYA:*
Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba?.
*AMSA:*
An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai.
Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:
An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Kada mace ta yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami_*.
Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu, Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta.
Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Ba Ya halatta ga mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta_* Bukhari da Muslim ne suka riwaito.
Amsawa: *_Sheikh Saleh al-Fauzan, Rahimahullah_*
A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 863.
✍🏼 Tattarawa:
*_Mal Umar Shehu Zaria_*