IDAN UBA BAI YIWA DANSA AKIKA BA RANAR BAKWAI, MENENE MAFITA ?
Tamabaya
Assalamu alaikum.
yaa shaikh (dr.) mutun ne Allah ta'ala ya bashi karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata hudu tukunna Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko ta fadi???
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi cewa ana yiwa abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.
Wasu malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya yi ranar 14 ko kuma ranar 21.
Duk wanda bai samu damar yiwa dansa Akika ba a kwanakin da aka ambata a sama, to babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya yi duk lokacin da ya samu dama.
AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya yiwa dansa a lokacin da Annabi S. a. w ya ambata, in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.
Allah ne mafi sani
Don neman karin bayani duba: Daka'iku Ulin Nuha 1/615.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/08/2017
Daga
ZAUREN FIQHUS SUNNAH