INA SO NA SAN SIFFOFIN JININ HAILA?
TAMBAYA:
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu,
Don tambaya gare ni Kan wani ruwa ke fitomin amma kuma ba jini bane .INA ganinsa kasa kasa .babu wari ko qarni tare dashi .INA ganinsa idan nayi Azumi ko nayi aiki sosai .se marata tayi ciwo .shine yake fitomin. Yaya Azumi na da sallah ta take shin zan cigaba da yansu ? .sannan yana fitomin wajan qarfe 3 na rana ne .
AMSA:
Wa alaikum assalam, mutukar ba jini ba ne, kuma ba baki ba ne, ba shi da karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi kyau ki je wajan likita don ya duba lafiyarki, saboda abin da kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da ya rasa daya daga cikin siffofinsa.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
9 Ramadan, 1437H
ku kasance da ISLAMIC SUNNAH a shafin mu na sada zumunta wato facebook
www.facebook.com/Islamicsunnah
ko ta whatsapp ga mai sha'awa sai a aiko da cikakken suna da state ta lambar mu