HUKUNCIN ZUBAN JINI KO DAUKEWAN SHI SANADIYAR SHAN MAGANI
Tambaya:
Assalamu alaikum, Menene hukuncin jinin da ya samu mace ta hanyar rashin shan maganin planing da ake sha wadda da zata tsallake kwana biyu bata sha ba jini zai zo mata amma data ci gaba da sha zai dauke shi ne nike son in san hukuncin shi.
Amsa:
Wa alaikumus Salaam, Lallai jinin da yake zo ma Mace sanadiyyar amfani da hanyoyin kayyade Iyali (Planning) shi ne asalin jinin Haila, dan haka a duk lokacin da mace ta yi amfani da wata hanya ta kayyade Iyali (planing) ta hanyar fitar da jini ko hana jinin fita, to babban abin da za ta lura da shi, shi ne, duk lokacin da jinin ya fito, hukuncin Haila ya hau kanta, ko da ba lokacin da ta saba haila ba ne in dai jinin ya zo to, hukuncin Haila ya tabbata a kanta.
Amma idan maganin ya hana jinin fita ne to, hukuncinta hukuncin mace mai tsarki ko da lokacin da ta saba Haila ne in dai jini bai zo ba to, babu hukuncin Jini a kanta domin hukuncin jini ba ya tabbata sai lokacin da jinin ya fito.
Allah Ya bamu ikon ganewa da gyarawa.
Amsawa:
Malam Ibrahim Jushi, Zamfara
01/07/2017.
Daga: ZAUREN FIQHUS SUNNAH