Mutumin Da Yayi Mafarki

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum mlan Allah yakarama ikhlasi amee rambayata itace shin menene hukun mutumin dayayi mafarki dadaddare to da asuba tayi sai yaje yayi sallah batareda yayi wankaba kuma bai canxa kayaba ko kuma da yayi wankan sai yaje yayi sallah dakayan bai cireba harma sallar axahar taxo kuma yaje yayi dakayan ajikinsa

AMSA
=====
👇
Wannan rashin wankan da baiyi ba har yaje yayi sallah a haka shine babban kuskure, sai dai ko inda wata larura ce da tasa baiyi wankan ba, Anan kenan zaiyi taimama, Sabida larurar da take tare dashi ta rashin ruwa ko tsananin sanyi ko kuma idan akwai wani rauni jikinsa wanda idan ya zuba ruwa za'a iya bashi matsala.
  Maganar kayan da yake jikinsa, bai wanke ba yaje yayi sallah dashi, babu wani abu.
Sabida akwai malaman da suke da hujjoji masu Karfi akan cewar maniyyi ba najasa bane.
  Hijjarsu ta farko, Bukhari da Muslim sun rawaito hadisi daga sahibatul kissa Ummuna Aisha Allah ya kara mata yarda tace, ina kankare maniyyi daga tufafin manzon Allah saw, sai yaje yayi sallah da wannan tufafin.
  Da wannan ne Malamai sukace maniyyi ba najasa bane, Sabida dole duk yadda aka kai da kankarewa sai an sami saura a wurin.
  Sannan kuma sukace, idan da maniyyi najasa ne, to mutum ma zai iya zama najasa kenan, tinda asalinsa kenan.
  Sannan bazai yiwuba, namiji yake zubawa matarsa najasa a jikinta ba.
 
Magana ta karshe, idan maniyyi ya bushe za'a kankareshi da farce, Wannan shine yafi chanchanta da Ace wankewa akayi, Sabida waccan ruwayar da ummuna aisha ta rawaito mana.
  Idan kuma yana danye ne bai bushe ba, za'a wanke shi.
Sabida hadisi da ummuna aisha Allah ya kara mata yarda tace  ina wanke maniyyi daga tufafin manzon Allah saw sai yaje yayi sallah, alhalin ana ganin sawun wurin da na wanke daga tufafin nasa.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)