Tambayoyi Uku

TAMBAYA
========

Assalamu alaikum,

Mallam ina da tambayoyi  kamar haka:

1)Naji wani malami yace :Ãdam saw wannan da muka fito daga yayansa shine na karshe Kafinsa anyi wasu Ãlãm -Ãlam bila adadin.

2)Qudubai Allah kadai yasan adadinsu daga cikinsu akwai Wanda Allah yabada tasarrufin kula da iskar da bayi suke shãka wasu tasarrufin abin da bayi suke ci wasu ruwan da ake shã dasauran aiyuka na rayuwar bayi.

3) Sannan mallam me Mallam Sharia sukace game da "AUTÃDU, NUJBA'U da kuma QUDBA'U shin mutanene, ko Aljanu ko shaidanu ko kuma malaiku?  Don naji wani malami yace sunayin magana da Allah.

Dafatan Mallam yana cikin koshin lfy.

AMSA
======

1. Gaskiya ba haka bane.
Allah ya halicci mala'iku kafin ya halicci duk wani mutum.
Farkon wanda Allah ya fara halitta daga cikin mutane shine Annabi Adamu.
Wannan shine maganar da ta dace da doron Alqur'ani mai girma da Kuma sunnar manzon Allah saw.
  Sannan akwai hadisin ceto, Wanda Anas Dan malam ya rawaito daga manzon Allah saw, inamul Bukhari da Muslim suka fitar dashi, manzon Allah saw yace, Bayi zasuje wurin Annabi Adamu, suce dashi, KAINE WANDA ALLAH YA FARA HALATTA A DORON DUNIYAR NAN, KUMA KAINE WANDA ALLAH YA HALITTA DA HANNUNSA, MUNA SON KA ROKA MANA ALLAH KOWA YASAN MATSAYINSA.
  kaga kenan wani ma yazo yace Maka akwai wasu halittar Alam a doron kasa kafin zuwan Annabi Adamu, Wannan ba haka bane. ISRA'ILIYYAT ne kawai.
 
2. Wannan ba haka bane gaskiya.

3. Wannna kuma ban sani ba, sai dai a tambayi manyan Malamai.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)