ZAN IYA BAWA ARNE GIDAN HAYA ?
Tambaya
Assalamu Alaikum
Don Allah yahalatta a gina gida abawa kiristan haya?
Amsa
Wa alaikum assalam
ya halatta mana, tun da Annabi S.A.W. yayi mu'amala da Yahudawa kuma ya mutu silkensa na yaki yana wajan Bayahude saboda Sha'ir din da ya amsa kamar yadda ya zo a hadisi ingantacce
Akwai gonakin Annabi S.A.W. da na sahabbai a wajan Yahudawan Khaibar inda suke aiki a cikinsu suke bawa musulmai rabin abin da ya fito na amfani kamar yadda ya tabbata a Sahihu Al-bukhari
In har an san zai yi barna ko sabon Allah a cikin gidan bai halatta a ba shi hayarsa ba, Allah madaukakin sarki yana cewa: "Kada ku rika taimakekeniya wajan aikata sabo" Suratu Al'ma'idah aya ta: 2.
A cikin Suratu Al-mumtahanah Allah ya yi bayani cewa: Ana iya kyautatawa kafirai a kuma yi musu adalci mutukar ba sa yakar musulmai, hakan sai ya nuna halaccin ba su haya
Allah ne mafi sani
Dr, Jamilu Zarewa
15/12/2017
Gà dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH sai ya yi saving wannan number +2348122248585 sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatsApp.Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.