ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI (INFECTION)

*_ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION._*
.
.
.
1) Rashin sanya pant.
2) Barin pant yay dauda sosai ba a canja ba. Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke.
3) Saka pant a jiqe da ruwa.
4) Yawan tsarki da ruwan sanyi.
5) Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yay yawa.
6) Rashin aski.
7) Wasa da gaba.
8) Yawan cin Danyar Albasa.
9) Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci.
10) Dadewa akan Masai ko toilet.
11) Rashin shan iska.
12) Musanyar tufafi.
13) Saduwa dai cutar.
12) Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.


*_ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA_*

1) Yana sa Rashin Sha'awa.
2) Yana sa ciwon mara mai tsanani.
3) Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.
4) Yana sa mace ta dinga jinin al'ada bakikkirin maiwari.
5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata.
6) Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.
7) Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.
8) Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.
9) Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.
10) Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.
11) In yay karfi yana hana mace haihuwa.
12) Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.
.
.
★Abin lura:-
★Idan mace tay magungunan Asibiti da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba, to ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce.

Rubutawa:- Sadiya Lawwal Abubakar
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)