MUMINI ƊAN GATA


MUMINI ƊANGATA

Allah Jalla wa Alā yace : 

( ثُمَّ نُنَجِّي رُسُلَنَا وَالَّذِينَ آمَنُوا كَذَٰلِكَ حَقًّا عَلَيْنَا نُنجِ الْمُؤْمِنِينَ ) سورة يونس (103)

Sannan Muna kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi imãni, kamar haka ne, haƙƙi ne a gare Mu, Mu kuɓutar da masu imãni.

Allah Ta'ala yace : 
( إِنَّ اللَّهَ يُدَافِعُ عَنِ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ خَوَّانٍ كَفُورٍ ) سورة الحج (38)

Haƙiƙa Allah Yanã bada kariya ga waɗanda suka yi ĩmãni. Haƙiƙa Allah bãya son dukkan mayaudari, mai yawan kãfirci.

Sa'adiy rahimahullah yace : gwargwadon imanin da bawa yake dashi zai samu kubuta daga abubuwan ƙi.

Allah kasamu cikin masu imani ka ƙawata imani a zukatanmu
Post a Comment (0)