FALALAR SALLAR JUMA'A

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

_*FALALAR SALLAR JUMA'A*_

_Insha *Allah* Zan Ambaci kadan daga cikin Hadisai Ingantattu Wadanda ukazo da Bayanin Falalar Sallar Juma'a daga Bakin *Annabi s.a.w*._

_*1-Imam Muslim* Ya Ruwaito Hadisi har zuwa kan *Abi Hurairata R.A* daga *Manzon Allah s.a.w* yace: (Salloli Guda Biyar na Farilla, Daga Juma'a Zuwa Juma'a, Ana kankare Zunuban da Akayi a tsakaninsu Idan an Nisanci Manya Manyan Zunubai)._
@ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 233 ).

_2-Daga *Abi Hurairata R.A* Daga *Annabi s.a.w* Yace: (Duk Wanda Yayi Wanka Sannan ya Taho Zuwa Sallar Juma'a Kuma ya Sallaci Abinda Yake da Iko (Ana Nufin Sallar Gaisuwar Masallaci) Sannan Yayi Shiru Lokacin da Liman yake Huduba har ya Gama Hudubarsa, Sannan Yayi Sallah Tare Dashi, An Gafarta Masa Zunubansa Na tsakanin Wannan juma'ar zuwa wata Juma'ar Har da Karin kwanaki Uku)._
@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 857 ) .

_*Imam Nawawy Allah* Yayi Masa Rahama Yake Cewa: {Ma'anar an Gafarta Masa Zunubansa na tsakanin Wannan Juma'ar Zuwa Wata Juma'ar har da karin kwanaki Uku, Lallai kyawawan Ayyuka Ana Ninka Ladarsu Har Sau Goma......"_

_3-Zuwa Masallacin Juma'a da Wuri Yanada Tarin Lada Mai Yawa._

_*Manzon Allah s.a.w* yana Cewa: (Wanda Yayi Wanka a Ranar Juma'a, Sannan ya Tafi Zuwa Masallaci a Farkon Lokaci, Yanada Lada kamar Yayi Sadaka da Rakumi. Idan Yaje a Sa'a ta Biyu kamar yàyi Sadaka ne da Saniya. Idan Yaje a Sa'a ta Uku kamar Yayi Sadaka ne da Rago. Idan Yaje a Sa'a ta Hudu kamar Yayi Sadakane da Kaza. Idan Yaje a Sa'a ta Biyar kamar yayi Sadakane da Dabino. Idan Liman Yazo Ya Hau kan Mimbari Sai Mala'ikun su Rufe Takardunsu su tsaya Suna Sauraran Khuduba)._
@ ﺭﻭﻯ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 841 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 850 ‏) ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ .

_4-Wanda ya tafi a kasa zuwa Sallar Juma'a Yana Samun Ladar Azumin Shekara Guda da tsayuwar dare na Shekara Guda ga Kowane taku._

_Daga *Ausi bn Ausi (ra)* Daga *Manzon Allah s.a.w* Yace: (Dukkan Wanda Yayi Wanka a Ranar Juma'a Wankan Juma'a, Yayi Sammako Yaje da Wuri, ya Zauna ya Saurari khuduba yayi shiru beyi Magana ba, Ya kasance yana da Lada ga Kowane Taku da Yayi Zuwa Masallaci, Yanada Ladar Azumin Shekara Guda da tsayuwar dare na Shekara Guda)._
@ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 410 ) .
ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﻓﻲ ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ ‏( 1/385 ) :
_Yana Cewa: *Imam Ahmad* Yana Cewa: (Wannan Wankan Yana Bayyana Mana Mustahabbine ga Mutumin Daya tara da Iyalinsa a Ranar Juma'a)._

ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
_Bayan Ya Jero Hadisan Falalar Sallar Juma'a Sai Yace: (Abinda Muka kawo na Falalar Juma'a Na Kankare Zunuban Juma'a Zuwa Wata Juma'ar da sauran falala. Hakan baya tabbata ga bawa sai ya Cika wadansu Sharudda Wanda suka zo Acikin Hadisan kamar:_

_✏ Yin Wanka da tsafta dan zuwa sallar juma'a._

_✏ Sanya tufafi mai kyau da sanya turare da shafa mai._

_✏ Da Tafiya cikin Natsuwa zuwa Masallaci._

_✏ Da barin Qetara Tsakanin Mutum Biyu da Rashin Cutar da Mutane a Masallacin._

_✏ Dayin Shiru Lokacin khuduba._

_*Allah Ne Mafi Sani*_

_*✍🏽Mustapha Musa*_

Post a Comment (0)