NAMIJI ZAI IYA KARA GASHI?

*NAMIJI ZAI IYA KARA GASHI !!!*
*Tambaya*

Assalamau alaikum Malam me hukuncin wanda ya qara gashi akansa irin wanda maza suke zuwa ana musu surgery ashuka musu gashin musamman ga masu sanko ko kuma waenda gashin kansu ke cincinyewa wai saboda su zama dai dai da sauran
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Bai halatta ga namiji ya kara gashi ba, saboda hakan canza halittar Allah ne.
Kasancewar Allah ya haramtawa mata kara gashi a cikin hadisai ingantattu duk da cewa suna tasowa NE a cikin kwalliya kamar yadda ayar Suratu Azzukruf ta tabbatar, hakan sai ya nuna namiji ne ya fi cancanta da haramcin, tun da shi ba'a yi shi don Ado ba.
Malamai suna cewa duka nassoshin da suke haramtawa mata kara gashi, to maza ma suna ciki, amma an kebance mata ne da haramcin saboda su ne suka fi yawan aikatawa.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
03/09/2017

Post a Comment (0)