TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum malam barka da warhaka Allah ya karawa malam lfy, Allah yayi jagora. Malam tambaya ce dani guda 2 Na farko malam akwai makaranta da muke zuwa amma a cikin masallaci ake koya mana karatun koda bamu da tsarki zamu iya shiga daukan karatu.
Tambaya na 2 malam akwai yar uwata data rasu kuma ana bin ta azumin bayan azumin tafara rashin lfy sai kuma Allah yayi Mata rasuwa malam mene hukunci. nagode Allah ya kara bashiru Allah ya saka DA mafificin alkhairi.
AMSA
======
👇
1. Baya Halatta ga Mai Haila ta shiga Masallaci ta Zauna Domin yin karatu ko Sauraron karutu din.
Sai dai ya Halatta ta shiga ta fito Domin Daukar wani Abu ko Ajiye wani Abu.
Ummuna Aisha Allah ya Kara Mata Yarda Tace, Manzon Allah saw yana umarta ta in dakko Abin sallah a Masallaci ko In kai Abin sallah Cikin Masallaci a Lokacin da ina Yin Haila. Sai dai ba na Zama a Cikinsa.
2. Wanda bai sami damar yin Azumi ba har Allah ya Karbi Rayuwarsa ana yin Azumin ba a gama ba, ko kuma Allah ya Karbi Rayuwar sa bayan ya gama Azumi ba tare da ya Warke ba. Babu Wani Ramuwar Azumi Akansa. Domin Ramuwa tana hawa Kan wanda ya sha Azumi ta dalilin Rashin Lafiya ko wani Ala'amari na daban Kuma ya warke daga baya.
Duk da Wasu Malaman Suna Ganin ma babu Damuwar Azumin Ramadan sai dai ko na Bakance Kawai.
Allah Shine Masani.
Allah shine Masani.
✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797