*🧕HIJJABI NA MUMMUNAI MATA NE 02🧕*
*🧕TAMBAYA AKAN HIJJABI🧕*
🧕Wasu dalilan da ke sa mace ta rufe jikinta sun haɗa da tsare mutuncin kan ta, kuma maza da mata zasu fi kimanta junansu idan suna rufe jikinsu akan buɗe tsiraicin junansu.
🧕Duk macen da ta ke saka hijjabi ta ke rufe kanta duk wanda ya ganta ze san cewa musulma ce mai kyakkyawar ɗabi'a. Mata da yawa wandanda suke rufe jikinsu sune masu mutunci da kamun kai; kuma wannan ce alamarsu ta zama mata Muminai.
🧕A matsayinta na mace mai kamun kai, mai mutunci, mai tsarki, ba ta taɓa yin rayuwar jima'i (zina), ko ƙulla hulɗa da sakin fuska ga kowa.
🧕Mace wacce ta ke rufe jikinta tana tsare farjinta daga alfasha (zina).
*✍Rubutawa/Fassarawa: Abdullah A Abdullah Abu Khadijat (أنصار السنة)*
15/05/1440.
20/01/2019.
Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
